Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Matasan Najeria da Benin sun ce, kasar Sin bata taba bata ranmu ba
2020-05-14 14:04:01        cri

Yanzu, dalibai wadanda suka fito daga kasashen Afirka suke karatu a wurare daban daban na kasar Sin sun yi yawa. Yanzu ga wani rahoto game da yadda matasa biyu wadanda suka fito daga kasashen Najeriya da Jamhuriyar Benin, kuma suke karatu a nan kasar Sin, sun yi aikin sa kai na bada taimako ga sauran dalibai wadanda suka fito daga sassan duniya daban daban a lokacin da ake dakile annobar COVID-19 a nan kasar Sin.

Dalibi Oscar Chijioke Nkwazema, wani saurayi ne daga kasar Najeriya, yanzu yana koyon ilmin na'urorin injiniya a reshen Wuhan na jami'ar koyon ilmin kimiyyar labarin kasa ta kasar Sin. Bayan barkewar annobar COVID-19 a kasar Sin, ya zauna a cikin jami'arsu dake Wuhan, kuma ya shiga wata tawagar masu aikin sa kai ta "Iron Man" dake kunshe da wasu dalibai wadanda suka fito daga kasashe 13, ciki har da wasu kasashen Afirka kamar Najeriya, Jamhuriyar Benin da Tanzania da Rwanda domin taimakawa hukumomin jami'ar wajen samar da kayayyakin yau da kullum ga dalibai 320 na kasashen duniya. A ganin Oscar Nkwazema, gwamnatin kasar Sin ta dauki matakai masu amfani wajen dakile annobar, yana kuma nuna godiya ga taimakon da malamai da hukumomin jami'ar suka samarwa daliban kasashen waje.

A watan Satumban shekarar 2019 ne, Oscar Chijioke Nkwazema ya isa birnin Wuhan ya fara karatunsa a birnin. A lokacin da yake zantawa kan batun annobar da ta barke ba zato, Oscar yana mai cewa, "Ya kamata in nuna godiya ga duk wadanda suka taimake mu, kuma ina godiya ga matakai daban daban da hukumomin jami'armu suka dauka wajen kwantar da hankalinmu. A kullum dalibai suna zaune a dakunansu ne. Ko da yake ya kasance da hadari sosai, amma malamanmu da wasu masu aikin sa kai sun dinga samar mana kayayyakin da dalibai suke bukata na yau da kullum, har ma da bada jinya ga wadanda suke bukata a kan lokaci."

Ba ma kawai hukumomin jami'ar ta samar da kayayyakin abinci da na kandagarkin annobar ba, har ma sun bada taimako ga dalibai domin kokarin kwantar da hankulansu.

Jami'ar ta kuma kafa wata tawagar masu aikin sa kai dake kunshe da wasu dalibai, ciki har da Oscar Nkwazema wadanda suka fito daga kasashe 13. Sannan a cikin wannan tawaga, an kuma kafa rukunoni daban daban, kamar su rukunin sayen abinci, da na sayen kayayyakin bukatun yau da kullum da rukunin rarraba kayayyaki ga dalibai, ta yadda za a iya tabbatar da ganin tawagar ta tafiyar da harkokin ba da taimako ga dalibai kamar yadda ya kamata.

Oscar Nkwazema ya ce, ko da yake masu aikin sa kai sun sha aiki sosai a cikin 'yan watannin da suka gabata, amma a ganinsa yana cike da farin ciki sosai.

"Ba a kullum ake iya samun damar yin aikin sa kai ba, ina farin ciki sosai sabo da dukkanmu zamu iya shawo kan annobar tare ta hanyar yin aikin sa kai. A gare ni, ina yin alfahari sosai domin na ba da taimako ga daliban makarantarmu."

Ban da Oscar Nkwazema, yanzu ga wani labari daban game da abokin karatunsa Tiando S. Damien wanda ya fito daga Jamhuriyar Benin, yake kuma karatun neman digiri na uku a reshen Wuhan na jami'ar koyon ilmin kimiyyar labarin kasa ta kasar Sin. Shi Tiando Damien ya ba da shawarar kafa wannan tawagar masu aikin sa kai, ya kuma nada sunan "Iron Man" ga wannan tawaga. Bayan barkewar annobar, Damien bai tafi ko'ina ba, sai dai ya zauna a cikin jami'ar ya yi aikin sa kai. Damien ya ce, kasar Sin kasa ce mai kwanciyar hankali wadda ke kokarin sauke nauyin dake bisa wuyanta. Kuma a ganin Damien, kasar Sin ta kasance tamkar wata mama wadda ba ta taba bata ransa ba.

"Ma'anar 'Iron Man' ita ce, muna da jarumtaka, ba mu ji tsoron wannan kwayar cuta. Kasar Sin ta kasance tamkar garinmu na biyu, saboda tana maraba da mu sosai. Ta kan burge mu. Sabo da haka, ina tsammani, ya kamata mu kafa wannan tawagar masu aikin sa kai."

Tiando Damien ya kuma bayyana cewa, sabo da ya zauna a birnin Wuhan, a lokaci mafi tsanani na dakile annobar, ya ji fargaba kadan, amma bayan ya ga matakan dakile annobar da gwamnatin kasar Sin ta dauka, ya kwantar da hankalinsa. Sabo da a ganinsa, kasar Sin kasa ce dake kokarin sauke nauyin dake bisa wuyanta. Ana samun kwanciyar hankali sosai a kasar Sin. Yanzu zaman rayuwa da tattalin arziki na birnin Wuhan na komawa yadda ake fata a kai a kai. Kasar Sin ba ta taba bata ransa ba. (Sanusi Chen)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China