Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Akwai yiwuwar mutane da dama a Turai sun kamu da COVID 19 a lokacin sanyi na bara
2020-05-12 13:13:12        cri

Ya zuwa yanzu, hukumomin kiwon lafiya, da cibiyoyin nazarin kimiyya na kasa da kasa, sun ba da sakamakon bincike dake nuna cewa, wasu mutane sun kamu da cutar COVID-19 a wasu kasashen Turai a lokacin sanyi na bara.

Ban da wannan kuma, wasu jami'ai, ko masana, sun shaidawa manema labarai cewa, mai yiwuwa cutar ta COVID-19 ta barke a kasashen tsakanin watan Satumba da na Disamba na bara, wato wasu watanni da dama kafin gabatar da rahoton bullar cutar a hukumance.

Asibitin Albert Schweitzer dake birnin Colmar na kasar Faransa, ya ba da sanarwa a ran 7 ga wata cewa, ya sake gudanar da bincike kan hotunan huhu 2,456 da aka dauka, na wasu marasa lafiya, tsakanin ran 1 ga watan Nuwamba na shekarar 2019 zuwa ran 30 ga watan Afrilu na bana, inda aka gano cewa, mai yiwuwa wasu mutane sun kamu da cutar tun a ran 16 ga watan Nuwambar bara.

Ranar 11 ga watan Maris, babban direktan hukumar shawo kan yaduwar cututtuka na Amurka(CDC) Robert Redfield ya amince cewa, akwai wasu mutanen da aka ce suka rasu sakamakon marisuwa, amma a hakika dai sun mutu ne sakamakon COVID-19. Idan an duba shafin Intanet na hukumar CDC na Amurka, ana iya ganin cewa, yanayin barkewar marisuwa na shekarar 2019 zuwa 2020, ya fara ne daga ran 29 ga watan Satumba na bara.

Mashahurin masanin aikin jiyya na kasar Italiya Giuseppe Remuzzi, ya shaidawa manema labarai na Amurka cewa, watakila COVID-19 ta bulla a kasar Italiya ne tun a watan Nuwamba, ko Disamba na bara. Abin da ya nuna cewa, cutar ta yadu a yankin Lombardia na Italiya, tun kafin ta bulla a kasar Sin.

Kwalejoji na jami'ar London na Birtaniya, da dai sauran cibiyoyin nazari, sun yi bincike kan alkaluman kwayoyin halittar cutar guda 7500, kuma sakamakon ya nuna cewa, asalin cutar ya fito ne tun a karshen shekarar bara, kuma a lokacin ne cutar ta yadu daga dabobbi zuwa Bil Adama. Wato ana iya cewa, COVID 19 ta yadu tsakanin Bil Adama tun daga karshen shekarar bara.

Ran 5 ga wata, mai magana da yawun hukumar lafiya ta duniya WHO Christian Lindmeier, ya ba da wata sanarwa game da cutar a birnin Geneva, inda ya ce, labarin da aka bayar na cewa COVID-19 ta bulla a kasar Faransa a watan Disamba na bara, ya canja fahimtarmu kan wannan cutar. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China