Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Lagos na shirin bude harkokin tattalin arziki sannu a hankali
2020-04-30 19:11:28        cri

Gwamnan jihar Lagos dake kudancin Najeriya Babajide Sanwo-Olu, ya ce sun shirya fara bude harkokin tattalin arziki sannu a hankali, duk da kasancewar jihar kan gaba a yawan masu fama da cutar numfashi ta COVID-19.

Lagos wadda ta shafe makwanni karkashin dokar zaman gida ga al'ummar ta, a cewar gwamna Sanwo-Olu, za ta samu damar sake bude shaguna a kowace rana tsakanin karfe 9 na safe zuwa 3 na yammaci.

Gwamnan na wannan tsokaci ne yayin zaman bayyana halin da jihar ke ciki na rana-rana da ya saba gabatarwa na jiya Laraba. Ya ce za a wajabtawa masu shiga kasuwanni daukar matakan kariyar lafiya, da na yin nesa-nesa da juna, tare da aiwatar da tsauraran matakan tsafta. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China