Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Geoffrey Onyeama ya jinjinawa gwazon Sin a fannin hadin gwiwar yaka da COVID-19
2020-04-24 20:15:52        cri

Ministan harkokin wajen Najeriya Geoffrey Onyeama, ya jinjinawa hadin gwiwar da kasar Sin ke yi da sauran sassan duniya, wajen yakar cutar numfashi ta COVID-19.

Ministan ya bayyana hakan ne, yayin zantawa da babban gidan rediyo da talabijin na kasar Sin CMG, yana mai cewa, baya ga raba bayanai da sauran sassa game da cutar da Sin ta yi, kasar ta kuma baiwa kasashe da dama tallafin kayan yaki da cutar, tare da tura kwararrunta zuwa sassan duniya don su taimaka.

Ya ce "A duk tsawon rayuwa ta, ban taba ganin inda aka killace birni ko kasa gaba daya ba. Amma an yi hakan a birnin Wuhan, kuma bayan yaduwar cutar zuwa sauran sassan duniya, karin kasashe da dama sun kwaikwayi salon dakile cutar da Sin ta aiwatar".

Onyeama ya kuma ce, Sinawa sun yi rawar gani, wajen aiwatar da matakan cimma nasarar dakile wannan annoba, kuma ko shakka ba bu, Sin ta samarwa duniya wani managarcin tsari na shawo kan wannan annoba. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China