Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta mayar da martani kan zargin da Amurka ta yi mata game da yaki da COVID-19
2020-04-22 21:14:36        cri
Ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin, ta yi watsi da zargin da Amurka ta yi, cewa dole Sin ta dauki alhakin yaduwar cutar numfashi ta COVID-19, wadda ta shafi sama da mutane miliyan 2.56 a sassan duniya daban daban.

Da yake tsokaci game da hakan, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar ta Sin Geng Shuang, ya ce zargin wata muguwar makarkashiya ce kawai, wadda ba za ta samu goyon bayan ko wace irin doka ba.

A ranar Talata ne dai jihar Missouri, ta zamo jihar farko a Amurka, wadda ta kai karar kasar Sin gaban kuliya, tana zargin ta da yin rufa rufa, game da matakan da ta dauka na dakile yaduwar cutar COVID-19. Mahukuntan jihar sun ce irin matakan da Sin ta dauka ne suka haddada mummunar karayar tattalin arziki da ta aukawa jihar.

Game da hakan, Mr. Geng ya ce wannan kara ce da ya kamata a yi watsi da ita. Kuma mataki ne da ba zai yiwa Amurka kyau ba, ya kuma sabawa matakan hadin gwiwa na kasa da kasa da ake aiwatarwa, wajen yaki da wannan annoba.

Daga nan sai ya jaddada matsayin kasar Sin, na taka muhimmiyar rawa wajen yakin da ake yi da wannan cuta a duniya baki daya, ciki hadda yadda kasar ta Sin, ta rika samar da bayanai, da raba su tare da hukumar lafiya ta duniya WHO, da ma sauran sassan duniya, ciki hadda ita kan ta Amurka. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China