Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin za ta kara fitar da kudade don ceto kananan kamfanoni
2020-04-22 11:05:55        cri
Gwamnatin kasar Sin ta bayyana kudirinta na bunkasa tattalin arziki a gabar da cutar numfashi ta COVID-19 ke yaduwa a duniya.

Firaministan kasar Sin Li Keqiang, shi ne ya bayyana haka, yayin da ya jagoranci taron majalisar gudanarwar kasar a jiya Talata. Inda ya nanata bukatar kara inganta hidimomin da suka shafi kudi don taimakawa tattalin arzikin kasar.

Taron ya kuma yanke shawarar daukar nauyin kimanta kwazon hukumomin kudi, da rage nauyin dake kan kanana da matsakaitan bankuna, ta yadda za a bunkasa hidimomin kudi da kananan kamfanoni.

Tun lokacin da COVID-19 ta barke, babban bankin kasar Sin, ya rage adadin kudadensa na ajiya sau uku a wannan shekara, inda ya samar da Yuan Triliyan 1.75, kwatankwacin dala biliyan 246.7 don taimakawa kananan sana'o'i.

Haka kuma, a wani mataki na rage wa kanana da 'yan kasuwa masu zaman kansu wani nauyi, taron ya yi kira da a sokewa irin wadannan kamfanoni dake bangaren bayar da hidima dake haya a gine-ginen gwamnati biyan kudin haya na watanni uku a watanni shida na farkon bana. (Ibrahim Yaya)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China