Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Masu sha'awar wasanni na ci gaba da motsa jiki a lokacin da ake tinkarar cutar COVID-19
2020-03-27 16:01:01        cri

Mai Sha'awar Guje-guje Song Dongliang

Sanin kowa ne cewa, wasan kwallon kafa da na kwando dukkansu wasanni ne da ake bukatar mutane da dama wajen yinsu, don haka barkewar cutar COVID-19 ta kawo babbar matsala ga masu sha'awar wadannan wasanni. Kamar yadda malam Wang Zixin ya fada, guje-guje shi ne tushen dukkan wasanni. Ko masu sha'awar guje-guje sun fuskanci matsala a yayin da ake tinkarar cutar COVID-19?

Song Dongliang, shugaban wani kamfanin daukar hotuna da bidiyo na birnin Beijing na kasar Sin ya shafe shekaru hudu zuwa biyar yana guje-guje. Saboda aikin da yake fama da shi a kowa ce rana, ya kan yin guje-guje har na tsawon kimanin kilomita biyar bayan da ya gama cin abincin dare. Ya ce, motsa jiki yana da muhimmanci ga lafiya da inganta karfinsa na tinkarar cututtuka.

Kafin barkewar cutar COVID-19, ya kan yin guje-guje a wurin yawon shakatawa a kowace rana. Amma yayin da cutar ta fara yaduwa matuka, an hana mutane shiga wurin yawon shakatawa, don haka bai iya yin guje-guje a waje ba. Maimakon haka, sai ya ci gaba da motsa jiki ta manhajar wayar salula kamar KEEP a cikin gida. Lokacin da aka farfado harkokin rayuwar jama'a a birnin, an sake bude wurin yawon shakatawa dake kusa da gidansa, inda ake duba yanayin zafin kowane mutum da yake son shiga wurin. A nan ne ya fara yin guje-guje a wurin tare da sanya abin rufe baki da hanci. Ya ce, yana motsa jiki na tsawon kilomita 5, amma saurin yin guje-guje ya ragu, saboda wahalar yin numfashi yayin da yake yin guje-guje tare da sanya abin rufe baki da hanci.

Malam Song ya kara da cewa, a kwanakin farko bayan da aka sake bude wurin yawon shakatawa, babu mutane da dama da suke yawo ko motsa jiki a wurin. Amma a halin yanzu, ana kara samun mutanen da suke zuwa wurin suna kuma motsa jiki. Ya ce,

"Da farko dai, yayin da nake yin guje-guje a wurin, na ga mutane biyu ko uku suna yawo ko motsa jiki a wurin. Amma a halin yanzu, a sakamakon nasarorin da aka samu wajen magance da hana yaduwar cutar, karin mutane sun fita waje tare da shiga wurin yawon shakatawa. Wasu sun kewaya, wasu sun yi guje-guje, wasu kuma sun yi wasan badminton, yayin da wasu kuma su ka motsa jiki tare da yaransu kanana."

A cewarsa, koda yake an kara samun mutane da suka fita waje suna yawo ko motsa jiki a wurin yawon shakatawa, amma babu cunkuso mutane, har yanzu ba a ga bayan cutar ba, don haka, ya kamata mutane su kiyaye matakan kare lafiya da aka tanada. Bayan da aka kawo karshen yaki da cutar, malam Song ya ce yana fatan zai iya tafiya wurare daban daban da yin yawon shakatawa, har ma a kasashen waje don kara yin walwala a waje ba tare da sanya abin rufe baki da hanci ba.

A halin yanzu, cutar COVID-19 ba ma kawai tana shafar Sinawa kawai ba, har ma tana yaduwa a dukkan duniya baki daya. Baya ga matakan yaki da cutar da gwamnatocin kasa da kasa suka gabatar, ya kamata jama'a su kiyaye motsa jiki don inganta lafiyarsu ta tinkarar cutar. Kamar yadda wadannan masu sha'awar wasannin motsa jiki na Sin guda uku suka fada, an soke yin wasannin dake bukatar mutane da dama a waje, da zabar sauran hanyoyin motsa jiki maimakonsu. Ya kamata a sanya abin rufe hanci da baki yayin da kuke a waje, da kaucewa shiga cunkuso mutane, da kuma wanke hannu sosai bayan da kuka koma gida daga waje. Muna fatan za a kai ga nasarar yaki da cutar, da kawo karshen ta cutar baki daya a duniya baki daya, ta yadda harkokin rayuwar jama'a na yau da kullumza su dawo cikin hanzari. (Zainab)


1  2  3  

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China