Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Masu sha'awar wasanni na ci gaba da motsa jiki a lokacin da ake tinkarar cutar COVID-19
2020-03-27 16:01:01        cri

Mai sha'awar Motsa Jiki Chen Rui

Chen Rui, wani manaja ne a sashen samar da kaya na kamfanin samar da kayayyakin kimiyya da fasaha ta yanar gizo na kasar Sin. Kafin abkuwar cutar COVID-19, ya kan yin motsa jiki a waje da kuma a cikin gida. A waje, ya kan buga wasan kwallon kwando a karshen mako sau daya a kowane mako, ya kan tafi filin wasan kwallon kwando na jami'ar dake kusa da gidansa don yin wasa tare da daliban jami'ar. Kana ya kan yi guje-guje sau biyu a kowane mako, gabili bayan ya gama aikinsa, ya kan guje-guje a cikin unguwarsa . A cikin gida kuma, ya kan yi mintuna 20 a kowa ce rana yana motsa jiki.

A yayin da yake makarantar firamare, ya yi shekaru 6, yana koyon wasan kwallon raga. Bayan da ya shiga makarantar midil, ya fara buga wasan kwallon kwando. A makarantar midil da kuma jami'a, yana daga cikin memban 'yan wasan kwallon kwando na makarantarsa. A ganinsa, motsa jiki wani bangare ne na rayuwarsa. Koda yake yana fama da aiki a kowace rana, amma duk da haka, bai daina motsa jiki ba. Ya ce motsa jiki yana kara masa lafiya, kana yana kawar masa da matsin lambar aiki ko na rayuwa.

Bayan barkewar cutar COVID-19, Chen Rui ya soke dukkan wasannin da yak e yi a waje kamar wasan kwallon kwando da kuma guje-guje. Ya ci gaba da motsa jiki ta manhajar wayar salula a cikin gida, inda yake motsa jiki kamar na tsawon mintuna 30 a kowace rana don kiyaye lafiyar jikinsa. Yanzu harkokin rayuwa sun fara dawowa kamar yadda aka saba, Chen Rui yana son dawo da yin guje-guje da ya saba sannu a hankali. Ya ce, ya kamata a sanya abin rufe baki da hanci a yayin da ake guje-guje, da rage yawan lokacin da ake yi a waje.

Chen Rui

Ya ce, a hakika kiyaye yin motsa jiki yana da ma'ana matuka a yayin tinkarar cututtuka. Ya ce,

"Na farko, kiyaye yin motsa jiki zai taimaka min wajen kiyaye lafiyar jikina, kana zai taimaka wajen hana kamuwa da cututtuka. Na biyu, lokacin da nake zaune a gida ba na fita waje, motsa jiki ya taimaka min wajen inganta rayuwata na yau da kullum yadda ya kamata. Don haka, lokacin da aka yi nasarar yaki da cutar, da maido da dukkan harkokin rayuwa, zan iya komawa harkokin na rayuwa cikin sauri ba tare da fuskantar matsaloli ba. Na uku kuma, bayan da aka hana fita waje, ba a samu damar yin motsa jiki, kuma nan da nan za a yi kiba. Motsa jiki yana hana yin kiba."

Chen Rui yana fatan za a kawo karshen cutar cikin hanzari, ta yadda za a dawo da dukkan harkokin rayuwar jama'a yadda ya kamata. Har a iya cin abinci da yin hira tare da abokai, da kuma maido da wasan kwallon kwando da sauran wasannin motsa jiki a waje.

1  2  3  

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China