Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Saliyo ta ayyana matakin ta baci don yaki da cutar COVID-19
2020-03-25 11:36:30        cri
Shugaban kasar Saliyo, Julius Maada Bio, ya ayyana matakin ta baci a matsayin wani yunkuri na yaki da cutar numfashi ta COVID-19.

Julius Maada Bio, wanda ya ayyana matakin a jiya, ya ce yadda cutar ke yaduwa a duniya babbar barazana ce ga rayuwar bil adama, kuma za ta iya kawo gagarumin tsaiko ga zamantakewa da tattalin arzikin kasar. A don haka, ya ce yanayin na bukatar managartan matakan kariya domin dakile yaduwar cutar a kasar.

Duk da cewa ba a samu rahoton wanda ya kamu da cutar a kasar Saliyo ba, gwamnati ta dauki matakai da dama na kandagarki, ciki har da haramta zirga-zirgar jiragen sama daga ketare. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China