Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
IOC: Za a tattauna yiwuwar jinkirta gasar wasannin Olympic ta Tokyo nan da makonni 4 masu zuwa
2020-03-23 10:31:02        cri

Jiya Lahadi, kwamitin shirya gasar wasannin Olympics na kasa da kasa wato IOC ya sanar ta shafinsa na Internet cewa, za a inganta shirya gasar wasannin Olympic ta Tokyo a shekarar 2020. Kana za a kammala tattauna yiwuwar jinkirta gasar nan da makonni 4 masu zuwa.

A wannan rana ne, Thomas Bach, shugaban IOC ya aika da wata wasika ga dukkan 'yan wasa ta shafin sada zumunta, inda ya bukace su, da su hada kai yayin da ake tinkarar matsala mafi muni da ba a taba ganin irinta a baya, wadda annobar cutar numfashi ta COVID-19 ta haifar. (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China