Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
IOC: Muna goyon bayan sashen wasannin Olympics na lokacin sanyi na Beijing
2020-02-18 11:52:31        cri

Jiya Litinin, manyan jami'ai na sashen wasannin Olympics na lokacin sanyi na birnin Beijing, da kwamitin wasannin Olympics na kasa da kasa na IOC, sun yi taro ta bidiyo, inda suka yi shawarwari kan ayyukan share fagen wasannin Olympics na lokacin sanyi na shekarar 2022 a birnin Beijing, ciki har da aikin sayen tikiti daga kasashen ketare, da aikin karbar baki na kasashen ketare, da aikin fadakar da jama'a da dai sauransu.

Bayan bullar cutar numfashi ta COVID-19 a kasar Sin, shugaban kwamitin IOC Thomas Bach, ya aika wata wasika ga kwamitin wasannin Olympics na kasar Sin, inda ya nuna imani kan kasar Sin, cewa tabbas barkewar cutar ba za ta dakatar da ayyukan shirya gasar wasannin Olympics na lokacin sanyi na birnin Beijing ba. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China