Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kwararrun ma'aikatan lafiya na kasar Sin sun samu kyakkyawan tarba a Italiya
2020-03-16 19:42:32        cri
Geng Shuang, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ya furta a yau Litinin cewa, bayan da tawagar kwararrun ma'aikatan lafiya da kasar Sin ta tura ta isa birnin Rome na kasar Italiya a ranar 12 ga wata, nan take ta fara taimakawa aikin dakile cutar COVID-19, abin da ya sa take samun karbuwa da yabo matuka daga al'ummun kasar Italiya. Har ila yau, wadannan kwararrun kasar Sin sun kuma taimakawa Sinawa dake da zama a kasar Italiya.

Tawagar da kasar Sin ta tura ta kunshi kwararrun aikin kiwon lafiya 9, wadanda suka tashi daga birnin Shanghai na kasar Sin, sa'an nan suka isa birnin Rome na kasar Italiya a ranar Alhamis da ta gabata, tare da dimbin kayayyaki da na'urorin da ake bukata. Daga bisani gwamnatin kasar Italiya ta kira taron manema labaru a ranar Jumma'a, musamman ma domin maraba da tawagar kwararrun kasar ta Sin. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba
Ga Wasu
v Italiya ta nuna godiya ga kasar Sin 2020-03-16 19:36:46

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China