Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta samu rahoton sabbin mutane 2,009 da suka kamu da cutar numfashi
2020-02-16 15:20:34        cri

Hukumar lafiyar kasar Sin ta samu rahoton sabbin mutane 2,009 da aka tabbatar sun kamu da annobar cutar numfashi ta novel coronavirus jiya, kana wasu sabbin mutane 142 sun mutu a ranar daga larduna 31 na kasar.

Kana a ranar Asabar, majinyata 219 ne suke cikin hali mai tsanani, yayin da aka sallami mutane 1,323 daga asibiti bayan sun warke daga annobar.

Baki dayan mutanen da suka kamu da cutar a fadin kasar Sin sun kai 68,500 ya zuwa ranar Asabar, kana jimillar mutane 1,665 ne cutar ta hallaka a fadin kasar, kuma mutane 9,419 ne aka sallama daga asibiti bayan sun warke daga cutar.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China