Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin ta jaddada goyon bayanta ga muradun Falasdinu
2020-02-12 10:20:06        cri

Zaunannen wakilin kasar Sin a MDD Zhang Jun, ya jadadda matasayar Kasar Sin na mara baya ga muradun al'ummar Falasdinu na dawo da halaltattun hakkokinsu, a daidai lokacin da Amurka ta gabatar da shirinta na zaman lafiya mai sarkakiya a kan yankin Gabas ta Tsakiya.

Zhang Jun, ya ce kasar Sin ta lura da sanarwar Amurka kan sabon shirinta na zaman lafiya a yankin gabas ta tsakiya da martanin Falasdinu da kungiyar kawancen kasashen Larabawa da kungiyar kasashe Musulmi da Sakatare Janar na MDD da sauransu.

Jakadan na kasar Sin ya shaidawa taron kwamitin sulhu na MDD kan shirin na Amurka cewa, har kullum, kasar Sin ta yi ammana kudurorin MDD da suka shafi batun da kuma matsayar da kasashen duniya suka dauka, kamar manufar kafa kasashe biyu da dawo da yankunan Falasdinu, muhimman tubala ne na warware rikicin Falasdinu, kuma dole ne a aiwatar da su yadda ya kamata.

Zhang Jun ya kara da cewa, kamata ya yi duk wani shiri irin wadancan, ya zo da batun tattaunawa da yarjejeniya bisa adalci, sannan ya bada gudummuwa ga samar da zaman lafiya mai dorewa. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China