Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An hallaka mutane 5 a yammacin kasar Nijar
2020-02-08 18:37:15        cri
Kafofin yada labarai na kasar Nijar sun ruwaito a jiya Jumma'a cewa, wasu 'yan bindiga da ba a san su wane ne ba, sun kai hari wani kauyen jihar Tillaberi dake yammacin kasar, a ranar 6 ga wata, inda suka hallaka fararen hula 5.

Wasu manyan jami'an jihar sun tafi kauyen a jiya Jumma'a, inda suka jajantawa iyalan wadanda suka rasu, da tunasar da su don su yi hattara, da hada gwiwa da hukumomin kasar, don kama mutanen dake kai mummunan hari tun da wuri.

A shekarun baya bayan nan, wasu kungiyoyi 'yan ta'adda sun yi ta kaddamar da hare-hare a yammacin kasar Nijar, inda ke iyaka da kasashen Mali, da Burkina Faso, tare da haddasa asarar rayuka da yawa. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China