Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Za a shirya taron kolin AU na 33 a watan Janairu
2019-12-24 20:18:29        cri
Kungiyar tarayyar Afirka AU) ta bayyana cewa, za a gudanar da taron kolin kungiyar karo na 33, wanda zai hallara shugabannin kasashe da gwamnatocin kasashe mambobin kungiyar daga ranar 21 ga watan Janairu zuwa 10 ga watan Fabrairun shekarar 2020. Taron zai gudana ne a hedkwatar kungiyar mai mambobi 55 dake Addis Ababa, fadar mulkin kasar Habasha.

Wata sanarwa da kungiyar ta fitar yau Talata na cewa, za a gudanar da taron kolin ne bisa taken " kawar da amon bindigogi: samar da yanayi mai kyau ga ci gaban Afirka"

Tashin hankali, yana daya daga cikin manyan kalubalen dake kawo cikas ga aiwatar da ajandar raya nahiyar nan da shekarar 2063, manufar kawo karshen matsalar karar bindigogi, ita ce kawo karshen dukkan yake-yake da fadan kabilanci, da tashin hankali mai nasaba da jinsi, rikice-rikice da kandagarkin kisan kiyashi a nahiyar nan da shekarar 2020. (Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China