Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Falastinawa sun zargi shirin zaman lafiyar Amurka a matsayin ayyana tashin hankali
2020-02-03 10:48:56        cri

Al'ummar Falastinawa sun sake nanata aniyarsu na yin watsi da shirin zaman lafiyar yankin gabas ta tsakiya wanda Amurka ta gabatar, inda suka bayyana shi da cewa "ayyana tashin hankali ne" ga al'ummar Falastinawa.

A cewar sanarwar da sashen diflomasiyya na kungiyar fafutukar kwato 'yancin al'ummar Falastinawa ta bayyana cewa, shirin Amurkar babbar barazana ce ga dorewar zaman lafiya wanda ya ci karo da dokokin zaman lafiya na kasa da kasa.

Sanarwar ta ce, yarjejeniyar ta kare dukkan muradun yahudawan Isra'ila, inda ta yi watsi da cikakkan ikon al'ummar Falastinawa.

Shirin na Amurka ya ci karo da hakikanin moriyar al'ummar Falastinawa tare da kwace musu dukkan ikon da suke da shi na mallakar matsugunansu, inda ya mayar da Isra'ila 'yar gaban goshi tare da hana Falastinawa duk wasu harkokin tafiyar da ikon yankunansu, da sararin samaniyar yankin, gami da tsaron yankunan teku, da kuma albarkatun kasa baki daya, in ji sanarwar.

Takardar bayanan ta ce, al'ummar Falastinawa a shirye suke su shiga dukkan wata muhimmiyar tattaunawar siyasa da aka shirya karkashin dokokin kasa da kasa, wadanda suka dace da kudurorin MDD, da yarjejeniyar zaman lafiyar kasashen Larabawa, kuma shugabannin Falastinawa a shirye suke su yi aiki da al'ummomin kasa da kasa don cimma nasarar hakikanin zaman lafiya daga tushe.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China