Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin ta yi alkawarin bada dala miliyan 1 ga 'yan gudun hijirar Falasdinu
2019-06-26 11:52:53        cri
Kasar Sin ta yi alkawarin bada dala miliyan 1 a bana, ga hukumar kula da jin kai ta MDD dake kula da 'yan gudun hijirar Falasdinu.

Mataimakin zaunannen wakilin kasar Sin a MDD Wu Haitao, ya ce kasar Sin na bada muhimmanci ga yanayin da 'yan gudun hijirar Falasdinu ke ciki, kuma ta damu da karancin kudin da hukumar ke fuskanta, yana mai cewa Kasar Sin za ta bada gudunmuwar dala miliyan 1 a bana.

Har ila yau, ya ce kasar Sin za ta samar da tallafi ga Falasdinawa ta hanyar hadin gwiwar kasashen biyu, ciki har da taimako ga shirye-shiryen agaji na yankunan kasashen.

Ya ce manufar kafa kasashe biyu, ita ce hanya mafi dacewa ta warware matsalar Isra'ila da Falasdinu. Wu Haitao ya kara da cewa, dole ne kasa da kasa su yi aiki bisa tushen shirin yarjejeniyar zaman lafiya ta Larabawa, da kudurorin MDD da suka shafi batun, domin samar da cikakken zaman lafiya da adalci mai dorewa ga matsalar, ta hanyar kafa kasar Falasdinu mai cikakken iko, karkashen iyakokin da aka shata na shekarar 1967 da kasancewar gabashin birnin Kudus a matsayin babban birninta. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China