Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Rundunar kawance ta sojojin Libya da Sudan ta tasa keyar bakin haure 107
2020-01-20 12:33:42        cri
Rundunar kawance ta sojojin Libya da Sudan, ta tasa keyar bakin haure 107 da aka gano a yankunan hamadar jihar Northern ta Sudan, dake kan iyakar kasar da Libya.

Kamfanin dillancin labarai na SUNA, ya ruwaito kwamandan dakarun kawancen na bangaren jihar Northern, Anwar Abdallah Nagodi, na cewa, an samu bakin hauren ne a cikin matsanancin yanayi, yayin wani aikin hadin gwiwa na dakarun kawancen, a yankin hamadar jihar dake kan iyakar kasashen biyu.

Ya ce an samarwa bakin hauren matsuguni da abinci da magunguna, sannan aka kwashe su zuwa Dongola, babban birnin jihar.

Kwamandan ya kuma lashi takobin dakarun kawancen, za su kara sa ido wajen yaki da bakin haure da safarar bil adama. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China