Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jakadan Sin ya bukaci a kara tuntubar juna kan batun sabunta shirin wanzar da zaman lafiyar MINURSO
2019-10-31 11:07:20        cri
Jiya Laraba jakadan kasar Sin a MDD yayi kira ga mambobin kwamitin sulhun MDD dasu cigaba da tuntubar junansu domin tabbatar da sabunta shirin kiyaye zaman lafiya na MDD a yammacin Sahara wato (MINURSO) a takaice.

Wu Haitao, mataimakin zaunannen wakilin kasar Sin a MDD, ya bayyana fatansa a cikin wani tsokaci da yayi bayan da mambobin kasashe 15 na kwamitin MDD suka kada kuri'ar amincewa da sabunta wa'adin aikin kiyaye zaman lafiyar zuwa ranar 31 ga watan Oktoban 2020.

Wu yace akwai bukatar a kara tuntubar juna game da tsawaita shirin zaman lafiyar na MINURSO a nan gaba domin samun cikakkiyar amincewar daukacin mambobin kan wannan kuduri.

Kana ya yabawa tsohon jami'in musamman na babban sakataren MDD, Horst Kohler. Ya bukaci a gaggauta nada magajin Kohler domin a samu damar dawowa kan teburin tattaunawa don cimma matsaya game da shirin wanzar da zaman lafiyar yankin yammacin Sahara.

Kudurin na ranar Laraba, ya jaddada bukatar a cimma nasarar samar da gamsasshen tsarin warware dambarwar siyasa a yankin yammacin Sahara.

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China