Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin za ta taka rawa mai ma'ana a yankin Gabas ta Tsakiya
2020-01-07 09:13:06        cri

Zaunannen wakilin kasar Sin a MDD, Zhang Jun, ya ce kasarsa za ta jajairce wajen taka rawa mai ma'ana, kan tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin Gabas ta Tsakiya da Gulf.

Zhang Jun, ya shaida wa manema labarai a hedkwatar MDD cewa, kasar Sin na bibiyar lamarin kuma abu mafi muhimmanci a yanzu shi ne, kare yanayin da ake ciki daga ta'azzara. Ya ce a matsayinta na mambar dindindin a kwamitin sulhu na MDD, kasar Sin za ta dauki managartan matakan diflomasiyya.

Mamban majalisar gudanarwa, kuma ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya tattauna ta wayar tarho da takwarorinsa na Rasha da Faransa da Iran, domin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin, sannan ya ce kasar Sin, na adawa da amfani da karfi cikin harkokin kasa da kasa.

Ya ce suna kira da Amurka da kada ta yi amfani da karfi ta hanyar da ba ta dace ba, sannan suna kira ga dukkan masu ruwa da tsaki su kai zuciya nesa tare da neman mafita ta hanyar hawa teburin sulhu.

Har ila yau, ya bukaci a girmama cikakken 'yanci da hadin kai da yankuna mallakar Iraki. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China