Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jakadan Sin ya bukaci a inganta aikin kiyaye zaman lafiya na MDD
2019-12-08 15:21:29        cri

Wakilin kasar Sin dake MDD ya yi kiran a inganta ayyukan wanzar da zaman lafiya na MDD ta hanyar aiwatar da dokokin da suka shafi aikin, da samar da karin kwarewa, da kyautata yanayin hadin gwiwa.

Tun daga shekarar 1948, dakarun shirin wanzar da zaman lafiya sun kasance a matsayin wata alamar MDD, wadanda ke kokarin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali da samarwa duniya kyakkyawar makoma. Sai dai a sabon yanayin da ake ciki a yanzu, da kuma sabbin kalubalolin da ake fuskanta, ayyukan kiyaye zaman lafiya na MDD suna bukatar dacewa da yanayin da ake ciki da kuma tabbatar da inganta ayyukan, Wu Haitao, mataimakin zaunannen wakilin kasar Sin a MDD shi ne ya bayyana hakan.

A lokacin wani taron duba hanyoyin da za'a inganta ayyukan wanzar da zaman lafiya na MDD, ya ce, ingantuwar ayyukan shirin wanzar da zaman lafiya yana da alaka ta kut da kut da aiwatar da dokoki, da samar da kwarewa, da kuma kyautata yanayin hadin gwiwa don cimma nasarar shirin.

Wakilin na Sin ya ce, Afrika ita ce babbar shiyyar da shirin wanzar da zaman lafiyar ke mayar da hankali. Shirin wanzar da zaman lafiya na kungiyar tarayyar Afrika yana taka muhimmiyar rawa domin warware matsalolin tsaro dake addabar Afrika. Kasar Sin tana tallafawa MDD wajen samar da dawwamman tsari da kuma kudaden gudanar da ayyukan wanzar da zaman lafiya.

Samar da zaman lafiya da tsaro ya kasance muhimmin batun da aka baiwa fifiko karkashin hadin gwiwar Sin da Afrika. Kasar Sin za ta ci gaba da samar da taimako ga kungiyar tarayyar Afrika domin tallafa mata wajen shirin kawo karshen karar tashin bindiga a Afrika zuwa karshen shekarar 2020.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China