Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Amurka ta fara shirin ficewa daga yarjejeniyar Paris
2019-11-05 09:54:05        cri

Sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo, ya bayyana cikin wata sanarwa a jiya Litinin cewa, kasarsa ta fara shirye-shiryen ficewa daga yarjejeniyar sauyin yanayi ta birnin Paris.

Idan ba a manta ba, a watan Yunin shekarar 2017 ne, shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da cewa, kasarsa za ta fice daga yarjejeniyar.

Bisa tanade-tanaden yarjejeniyar, kasashen da suka sanya hannu, za su bukaci ficewa daga cikinta ne shekaru uku bayan ta fara aiki, wato ranar 4 ga watan Nuwanban shekarar 2019, kuma shirin ficewar zai fara aiki ne shekara guda daga lokacin da ta sanar da janyewar. Hakan na nufin kasar Amurka za ta fice daga yarjejeniyar a hukumance a ranar 4 ga watan Nuwanban shekarar 2020.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China