Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
AU ta bayyana zaben da aka yi a Guinea Bissau a matsayin sahihi
2020-01-01 15:14:37        cri

Tawagar sa ido kan harkokin zabe ta Tarayyar Afrika AU, da aka tura kasar Guinea Bissau, ta bayyana a jiya cewa, zaben shugaban kasar da aka yi, ya gudana cikin lumana da tabbatar da tsaro.

Cikin kwarya-kwaryar rahotonta, tawagar ta ce an kada kuri'a cikin kwanciyar hankali da lumana. Sannan, ta taya al'ummar kasar Guinea Bissau murnar samun ci gaban zabe da kuma jan ragamar harkokin zaben kasar.

AU wadda ta tura manyan jami'ai domin sa ido kan zaben Guinea Bissau karkashin jagorancin tsohon firaministan kasar Sao Tome and Pricipe, Joaquim Raphael Branco, ta jaddada cewa, zagaye na 2 na zaben da aka yi ranar 29 watan Disamba, gagarumar nasara ce ga tarihin siyasar kasar, tana mai cewa al'ummar kasar sun kada kuri'a cikin kwanciyar hankali.

Tawagar wadda ta ce wakilan 'yan takara da galibinsu matasa ne, sun kasance a dukkan rumfunan zaben da suka ziyarta, kuma sun kiyaye ka'idoji. Tana mai cewa, sun kasance dauke da jerin bayanan masu kada kuri'a, wanda ya ba su damar bibiya da tantance tsarin kada kuri'a. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China