Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An kammala zagaye ne biyu na zaben shugaban kasar Guinea-Bissau lami lafiya
2019-12-30 10:12:12        cri
Mai magana da yawun hukumar zaben kasar Guinea-Bissau(NEC) Felisbeeta Moura Vaz, ta sanar a jiya Lahadi cewa, an rufe dukkan tashoshin zaben shugabancin kasar zagaye na biyu da misalin karfe 5 na yammacin jiya agogon wurin.

Vaz ta kuma karyata zargin tabka magudi da ake yayatawa a kafofin sada zumunta, inda ta bukaci 'yan takara da kada su bayyana sakamakon zaben, tun da a cewarta " hukumar zaben kasar ce kadai ta ke da ikon yin haka".

Tun da misalin karfe 7 na safe ne dai aka bude rumfunan zabe, inda masu kada kuri'a 761,676 da aka yiwa rijista a kasar, za su zabi sabon shugaban kasa, tsakanin Domingos Simoe Pereira da Umaro Sissoco Embalo.

Da yake Karin haske game da zaben, shugaban tawagar kungiyar tarayyar Afirka dake sa-ido a zaben, Joaqium Rafeal Branco, ya bayyana jiya da rana cewa, ba a samu rahoton wata matsala da safe ba, ya kuma yaba da halin ya kamata da 'yan kasar ta Guinea –Bissau suka nuna a lokacin wannan zabe.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China