Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An samu matukar fitar masu kada kuria a zaben shugaban Guinea-Bissau
2019-11-25 09:30:36        cri

Zaben shugaban kasar Guinea-Bissau yana ci gaba da gudana cikin kwanciyar hankali, sannan an samu matukar fitar masu kada kuri'a, hukumar zabe mai zaman kanta ta kasar Guinea-Bissau (NEC) ta sanar da hakan da yammacin ranar Lahadi.

Haka zalika, shugaban tawagar masu sanya ido a zaben na kungiyar tarayyar Afrika, Joaquim Rafael Branco, ya tabbatar da wannan ci gaban da aka samu, kuma ya yabawa irin halayyar da masu kada kuri'u a zaben na Guinea-Bissau suka nuna.

A cewar wakilin kamfanin dillancin labarai na Xinhua wanda ya ziyarci rumfunan zaben, an ga dogayen layuka a rumfunan jefa kuri'un a Bissau, kuma wasu tsirarun rumfunan zabe ne ba'a bude su a kan lokacin da aka tsara ba.

Wata mai shirya fina finai Flora Gomes ta fadawa Xinhua bayan ta jefa kuri'arta a Bissau cewa, suna son zaben shugaban kasar da zai taimake su wajen tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankalin kasar.

Daya daga cikin 'yan takarar mafi farin jini, tsohon firaministan kasar Domingos Simoes Pereira, dan takarar dake samun goyon bayan jam'iyyar PAIGC, ya bukaci masu kada kuri'a da su yi ruwan kuri'u, a jawabin da ya gabatar bayan jefa kuri'arsa a kusa da gidansa.

Shugaban kasar mai ci kuma dan takarar indifenda Jose Mario Vaz, ya kada kuri'arsa a kusa da fadar shugaban kasar dake Bissau. Ya bukaci masu kada kuri'a da su yi fitar dango don halartar rumfunan zaben ta yadda za su sauke nauyin dake bisa wuyansu a matsayinsu na 'yan kasa.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China