Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Nasarorin da Sin ta samu a fannin kare hakkin dan adam sun samu yabo a taron MDD
2019-10-27 16:24:36        cri

An yaba da irin nasarorin da kasar Sin ta samu a fannin kare hakkin dan adam a lokacin taron MDD game da 'yancin tabbatar da ci gaba wanda tawagar wakilan kasar Sin a MDD ta karbi bakuncin taron a ranar Juma'a.

Daga cikin mahalarta taron, akwai jakadun kasashen Belarus, Cuba, da Najeriya, da manyan jami'an sashen bunkasa tattalin arziki da jin dadin al'umma na ofishin kare hakkin dan adam na MDD, da wakilai daga ofisoshin jakadancin kasashe 40 da suka hada da Rasha, Italiya, Singapore, Indiya da Algeriya.

Masu gabatar da jawabai a wajen taron, sun gamsu cewa, hakkin samar da ci gaban dan adam muhimmin ginshiki ne na aiwatar da ajandar samar da dawwamamman ci gaban bil adama nan da shekarar 2030 na MDD. Sun yi matukar gamsuwa bisa tsarin kare hakkin bil adam da kasar Sin take gudanarwa da irin nasarorin da ta cimma, sun yabawa nasarorin da kasar Sin ta samu a fannonin bunkasa tattalin arziki, da yaki da fatara, sun ce kasar Sin ta baiwa duniya al'ajabi, kuma hakan ya sharewa sauran kasashe masu tasowa a duniya hanya da su koyi darasi kan batun kare hakkin bil adam daga shirin na kasar Sin.

Zhang Jun, zaunannen wakilin kasar Sin a MDD, ya bayyana cewa gwamnatin kasar Sin ta ba da fifiko matuka kan batun raya kasa da 'yancin rayuwa, da kuma ci gaba a matsayin tushen kare hakkin dan adam.

Jakadan ya ce, kasar Sin tana baiwa sauran kasashe masu tasowa taimako da zuciya daya domin su raya ci gaban kansu, ba tare da gindaya sharadin siyasa ba.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China