Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Filin wasa na Yuan 100
2019-11-29 09:45:16        cri

A garin Xiapu dake lardin Fujian na kudu maso gabashin kasar Sin, akwai wani filin wasa dake kan rairayin bakin teku na musamman, sunansa shi ne "Filin wasa na Yuan 100".

Wani mutum mai suna Chen Longqiang ne ya kafa wannan filin wasa, wanda yake da burin horar da kananan yara masu sha'awar wasan kwallon kafa a garin. Wadannan yara suna buga wasan kwallon kafa tare da shi a kan wannan filin wasa na musamman, da jin dadin wasan sosai tare da samun kyakkyawan maki a wannan fanni. Har ma wasu yara sun fita daga kauyen don canja rayuwarsu ta wasan kwallon kafa.

Chen Longqiang mai shekaruna 33 a duniya, malami ne dake koyar da wasan kwallon kafa a makarantar firamare ta hudu dake garin Xiapu. Ya zauna a kauye a lokacin kuruciyarsa, inda ya fara buga wasan kwallon kafa a yayin yake makarantar firamare, kuma yana son wasan sosai.

Yayin da yake da shekaru 17 a duniya, ya bukaci koyon fasahohin samar da kayayyakin marmara don bada taimako ga kantin kayan marmara na mahaifinsa. A sakamakon hakan, ba shi da lokacin buga wasan kwallon kafa a lokacin.

A shekarar 2016, saboda karancin ciniki a kantinsa, Chen Longqiang ya rika yawo a rairayin bakin teku, har ya kai ga gano wasu kananan yara dake buga wasan kwallon kafa a rairayin bakin tekun. Hakan ne kuma ya sake farfado da sha'awarsa ta wasan kwallon kafa, kuma ya buga wasan tare da yaran a kan rairayin.

Chen Longqiang ya bayyana cewa, da farko dai babu sandunan raga na wasan kwallon kafa a rairayin bakin teku, saidai ya yi amfani da kayan soso da duwatsu a matsayin turakan gola biyu na wasan. Sai dai kuma abu ne mai wuya a bambanta ko kwallo ta shiga raga ko a'a. Bayan gama horaswarsu a wata rana, a kan hanyar koma gidansa, Chen Longqiang ya gano wani kantin sayar da bututun roba, lamarin ya maida Chen Longqiang ya yi tunani cewa, ana iya kafa turakan gola guda biyu ta hanyar amfani da bututun roba.

"Na auna fadi da tsayin turakan gola na wasan kwallon kafa, sa'an nan na sayi bututun roba guda shida don kafa turakan gola biyu. Yana da sauki kafa su a yayin da za a fara buga wasan, da kuma ajiye su bayan da aka gama horaswa. Tun da muka samu irin wadannan turakan gola biyu, filin wasanmu ya yi kamar hakikanin filin wasan kwallon kafa. Yawan kudin da aka kashe wajen sayen su bai wuce Yuan 100 kacal ba."

Don hakan, filin wasa na Yuan 100 ya fito.

Tun bayan kafa filin wasa na Yuan 100, karin kananan yara suna zuwa don buga wasan kwallon kafa tare da Chen Longqiang. Don haka, Chen Longqiang ya kafa wata kungiyar wasan kwallon kafa mai suna "Changfeng", wato iska a kan teku da Hausa. Wannan suna ya zo daga wakar mashahurin mai rubuta wakoki na daular Tang na kasar Sin Li Bai, ma'anarsa ita ce koda yake ana fuskantar kalubale, amma an yi imani da cewa za a cimma buri a nan gaba ta hanyar yin kokari. Ma'anar ta dace da yanayin kungiyar Chen Longqiang.

"Mu kan yi horaswa a kan rairayin bakin teku tare da fuskar iska, shi yasa muka yi amfani da 'Changfeng' a matsayin sunan kungiyarmu, wanda ya dace da yanayinmu a yanzu. Muna son samun kyakkyawan maki ta hanyar yin kokarinmu na horaswa."

Akwai yara fiye da 10 a cikin kungiyar "Changfeng", shekarunsu suna daban daban. Ban da yanayin mahaukaciyar guguwa, su kan buga wasan kwallon kafa a kan filin wasan har na tsawon awoyi biyu ko uku. A lokacin da aka gama horaswa a kowace rana, Chen Longqiang na kai dukkan yaran zuwa gidajensu bi da bi. Kafin ya kammala kai su gida kuwa, lokaci zai zarce karfe 10 na dare. Ga wadannan yara, Chen Longqiang ba ma malaminsu kawai ba ne, shi wani abokin su ne, yaran da yake koyarwa su kan kira shi da sunan "dan uwa Long".

Amma mutane a kewayensu ba su fahimci dalilin da ya sa baligi kamar Chen Liongqiang zai rika buga wasan kwallon kafa tare da kananan yara ba. A ganinsu, Chen Longqiang ba shi da aikin yi. Har ma iyalansa ba su amince da hakan ba a farko. Amma Chen Longqiang ya kiyaye yin horaswa tare da yara, kana yaran da yake koyarwa suna son wasan kwallon kafa sosai, kana a gasanni suna samun maki mai kyau, daga baya kuma mutane sun fara nuna amincewa gare su. Haka kuma iyalan Chen Longqiang sun fara canja ra'ayinsu, suna ganin cewa, hanyar da Chen Longqiang yake bi hanya mai dacewa. 'Yar innar Chen Longqiang mai suna Li Fang ta bayyana cewa,

"Da farko, mun ki amince da shi, domin yana buga wasan kwallon kafa amma bai gudanar da aikin kansa ba. Amma a halin yanzu, mun canja ra'ayinmu, mun gane a hakika dai wasan kwallon kafa yana samar da taimako ga kananan yara."

Yaran da Chen Longqiang yake koyarwa suna son buga wasan kwallon kafa a kan rairayin bakin teku sosai, wasan yana kawo jin dadi gare su, kana ya samar da hanyar yin rayuwa ta daban gare su. A cikin wasu shekarun da suka gabata, yaran kungiyar Changfeng da dama sun zama muhimman membobin kungiyar wasan kwallon kafa ta makarantunsu, har ma wasu daga cikinsu sun shiga kungiyar wasan ta garin Xiapu.

An haifi Chen Xiaohong a shekarar 2005, wanda ya fara yin horaswa tare da Chen Longqiang a aji na hudu na makarantar firamare. A sakamakon kwarewarsa da kokarinsa, an shigar da Chen Xiaohong a cikin kungiyar wasan kwallon kafa ta garin Xiapu, a yayin aji na shida na makarantar firamare nasa. Kana domin wasan kwallon kafa, an shigar da shi zuwa makarantar midil mai kyau ta garin. Chen Xiaohong ya ce, ba ma fasahohin wasan kwallon kafa da malam Long ya koya masa kawai ba, hatta ma ya koya masa yadda za a cimma burinsa ta hanyar yin kokari. Chen Xiaohong ya ce,

"Na koyi fasahohin buga wasan kwallon kafa daga wajen malam Long, ina da burin zama dan wasan kwallon kafa, malam Long shi ma nuna mini yadda zan cimma buri na. A halin yanzu, zan koma buga wasan kwallon kafa tare da shi idan ina da lokaci."

Don koyar da yara fasahohin wasan kwallon kafa mai kyau, Chen Longqiang wanda bai samu horo bisa tsarin wasan ba, yana kiyaye yin horaswa har na tsawon awoyi biyar ko shida, tare da koyon fasahohi daga bidiyo ta yanar gizo. Bisa kokarinsa, Chen Longqiang ya samu digiri E da kuma digiri D na mai horaswa kan wasan kwallon kafa, kana ya samu damar shiga makarantar firamare ta hudu ta garin Xiapu a matsayin malamin koyar da wasan kwallon kafa.

Bayan da ya zama malamin makarantar firamare, Chen Longqiang bai manta da yaran da yake koyarwa a kan rairayin bakin teku ba, ya kan koma filin wasa na Yuan 100 ya buga wasan kwallon kafa tare da yara a kowace rana bayan da ya gama koyarwa a makaranta. Ya ce, yana jin dadin buga wasan kwallon kafa tare da yaran da yake koyarwa, ya ga yadda yaran suke yin kokari don cimma burinsu, wanda ya burge shi sosai, yana fatan wasan kwallon kafa zai kawo musu mai babbar ma'ana a rayuwarsu. Ya ce,

"Ina son kara koyar da kananan yara fasahohin wasan kwallon kafa, da yada wasan a garinmu, ya yi musu jagoranci, su kara samun kwarewa mai kyau a gasanni. Wasu daga yaran da suka buga wasa tare da ni, suna son zama 'yan wasan kwallon kafa a nan gaba. Haka zalika kuma, ko da yaran ba su zama 'yan wasan kwallon kafa a nan gaba ba, duk da haka akwai fatan wasan zai yi musu babbar ma'ana a rayuwarsu, da samar musu da gudummawa a zamantakewar al'umma."

A kowace rana, ana iya ganin malam Long da yaran kungiyar "Changfeng" suna buga wasan kwallon kafa a filin wasa na Yuan 100 dake kan rairayin bakin teku. A ganin Chen Longqiang, yaran da yake koyarwa, za su fita daga kauyensu, da tashi zuwa wurare masu nisa. Yana fatan a nan gaba yaran za su tuna da shi, su komo garin da sake buga wasan kwallon kafa tare da shi. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China