Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Dawowar Lippi na tattare da kalubalen kai tawagar Sin tudun mun tsira
2019-06-07 19:12:18        cri


Dawowar koci Marcello Lippi kasar Sin a matsayin babban kofin kungiyar kwallon kafar kasar na tattare da kalubale, duba da cewa babban burin kasar ta Sin shi ne lashe kofin kwallon kafa na duniya.

Lippi wanda ya taba daga kofin na duniya a baya, ya sake samun damar dawowa horas da 'yan wasan Sin a karo na biyu. To sai dai kuma a wannan karon ma aiki sa na cike da kalubale.

Kocin dan asalin kasar Italiya mai shekaru 71, ya sha fama da aikin horas da 'yan wasan na Sin a zangon shekaru biyu da ya yi a baya, ba tare da cimma cikakkiyar nasara ba, inda a wancan lokaci ya gaza kai kasar ga samun gurbin buga gasar kwallon kafar duniya wadda hukumar FIFA ke shiryawa na shekarar 2018 da ta gabata.

Bayan hakan ne kuma koci Lippi ya sake gamuwa da wata rashin nasarar, yayin da kungiyar kasar Iran ta doke Sin da ci 3 da nema, a watan Janairun bana, yayin wasan kusa da kusan na karshe, na cin kofin nahiyar Asiya. A wannan lokaci ne kuma ya yanke shawarar ajiye aikin sa.

Bayan tafiyar Lippi sai hukumar kwallon kafar Sin CFA, ta maye gurbin sa da dan wasan da ya horas wato Fabio Cannavaro a watan Maris. Sai dai kuma ba da jimawa ba, Cannavaro ya ci karo da rashin nasara har karo biyu a jere, a wasannin da kungiyar ta Sin ta buga wanda hakan ya tabbatar da cewa shi ma dai ya gaza. Wannan ne kuma ya sa hukumar ta CFA ta yanke shawarar sake dawo da Lippi.

Duba da dadewar sa yana horas da kungiyar kasar Sin tun daga shekarar 2012, Lippi ya zamo wani kwararre da ya lakanci salon kwallon kafar Sin. Koci ne wanda baya bukatar yin wani shiri sabo, a aikin sa na tsarawa kungiyar dabarun samun gurbi, cikin kungiyoyin Asiya da za su buga zagaye na biyu, na neman gurbin buga gasar cin kofin duniya da za a yi a shekarar 2022 a Qatar, wasannin da za a buga cikin watan Satumba.

Dama dai a baya, Lippi ya taba jagorantar kasar Italiya, inda ta lashe gasar cin kofin duniya na shakarar 2006, ya kuma jagorancin kungiyar Juventus inda ta lashe kofin zakarun turai na UEFA, kana ya jagoranci kungiyar Guangzhou Evergrande lashe kofin kalubale na Sin ko "Chinese Super League" har karo uku, kana a shekarar 2013 ya jagoranci kungiyar ta lashe kofin kalubale na AFC. Hakan ne kuma ya baiwa Lippi ikon da ake fatan zai yi amfani da shi, wajen kai tawagar kwallon kafar Sin ga babban sakamako.

Cikin wata sanarwa da hukumar CFA ta fitar game da sake nadin Lippi, ta ce "lokacin da Lippi ke rike da ragamar babbar kungiyar kasar Sin, 'yan wasan sun nuna kuzari da kwazon cimma nasara,".

Yanzu dai babban aiki da ke gaban Lippi shi ne jagorantar tawagar Sin, wadda a yanzu haka ke matsayi na 74 a jadawalin hukumar FIFA, ta yadda za ta samu gurbin buga gasar cin kofin duniya na shekarar 2022 da za a yi a Qatar.

Sai dai yayin da yake fuskantar wannan aiki, wani kalubale da zai iya fuskanta shi ne, yadda wasu daga tsofaffin 'yan wasan kungiyar irin su Zheng Zhi ke yin ritaya, yayin da su kuma matasan 'yan wasan kungiyar ba su da cikakkiyar gogewar tunkarar wannan babban aiki. Kaza lika kuma hukumar FIFA ta yi watsi da shirin ta, na kara yawan kungiyoyin da za su rika buga gasar cin kofin duniya da take shiryawa daga 32 zuwa kungiyoyi 48, yayin gasar da za a yi a Qatar, wanda hakan ke nuna cewa, dole ne Sin ta yi yakin kwatar kai, domin samun gurbin shiga gasar daga nahiyar Asiya.

Aiki dake gaban Lippi na farko shi ne, shirya tawagar Sin da za ta tunkari kasashen Philippines da Tajikistan, a wasannin sada zumunta da za a buga a birnin Guangzhou na Sin cikin watan nan na Yuni. Dole ne Sin ta lashe wadannan wasanni biyu, muddin tana fatan shiga kasashe 8, na sahun gaba da za a kadawa walwa-walar zabo su, domin buga zagaye na biyu na kasashen dake neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya na Qatar na shekarar 2022.

Baya ga batun shiga gasar cin kofin duniya, sabuwar kwantiragin Lippi da hukumar CFA, ta kuma kunshi aikin shirya kungiyar da za ta zama mai masaukin baki, a gasar cin kofin kungiyoyin kasashen Asiya ta shekarar 2023. Bayan Koriya ta kudu ta janye daga neman karbar bakuncin gasar, Sin ce kasa ta karshe da ta nuna sha'awar karbar bakuncin gasar ta AFC, wadda kulaflika 24 ke bugawa.

A shekarar 2004 dai Sin ta kai wasan karshe na cin kofin zakarun Asiya, lokacin da kasar ta karbi bakuncin gasar, wanda ko shakka ba bu, Sinawa masu sha'awar kwallon kafa, za su so sake ganin tawagar "Team Dragon" ta kasar, ta kai ga lashe gasar nahiyar a gida a shekarar 2023 dake tafe.(Saminu Alhassan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China