Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Huldar dake tsakanin Sin da Amurka a idon Henry Kissinger
2019-11-24 16:12:13        cri

A kwanakin baya, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da tsohon sakataren harkokin wajen kasar Amurka Henry Kissinger, a nan birnin Beijing. Inda Kissinger ya halarci wasu bukukuwa tare da gabatar da jawabi cewa, dole ne a yi kokarin fahimtar al'adun kasar Sin, kafin a samu fahimtar manufofin kasar.

Yayin da yake amsa tambayar da aka yi masa cewa, " Ko Sin da Amurka za su fara yakin cacar bakin da aka taba yi tsakanin kasashen Amurka da USSR?", Kissinger ya ce wannan yanayi ka iya zama abun gaskiya ne, inda kasashen Amurka da Sin sun fara kin jinin juna sosai, sa'an nan su yi kokairn neman samun amincewa daga kasashe daban daban. A cewar tsohon jami'in, kasar Sin wata babbar kasa ce mai tattalin arziki, kuma tana da alaka sosai da tattalin arzikin Amurka. Don haka idan an samu babban rikici tsakanin kasashen 2, yanayi zai fi muni, idan an kwatanta da yadda kasashen Turai suke a baya. A ganin mista Kissinger, ko da yake akwai bambanci tsakanin Amurka da Sin, amma wannan bambanci bai kai haddasa yaki tsakanin kasashen 2 ba.

Dangane da takaddamar ciniki tsakanin kasashen 2, mista Kissinger, ya ce yanzu a kan yi shawarwari ta fuskar tattalin arziki da ciniki tsakanin kasashen 2. Wannan, a cewarsa, mafari ne ga wani shawarwari mai muhimmanci a fannin siyasa da za a gudanar tsakanin kasashen 2 a nan gaba. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China