Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin za ta fara binciken duniyar Mars a shekara mai zuwa
2019-10-08 14:15:06        cri
Babban masanin kimiyya da harkokin bincike mai zurfi a fannin sararin samaniya na kwalejin nazarin fasahar sararin samaniya na kasar Sin, Ye Peijian ya bayyana a kwanan baya, cewa a shekara mai zuwa, kasar Sin za ta fara yin bincike a duniyar Mars, kuma za a kara wa na'urar binciken wata sabuwar karamar na'ura don kaucewa wata matsala, idan aka katwanta da na binciken duniyar wata.

Ye ya kara da cewa, kasar Sin ta riga ta soma aikin kera na'urar binciken duniyar Mars, kuma za a harba ta a shekara mai zuwa. Wannan binciken da za a yi zai cimma wasu manufofi guda uku a fanin kimiya na farko, zai kammala aikin duba da bincike kan duniyar Mars baki daya. Na biyu, na'urar binciken za ta sauka a Mars. Na uku kuma na'urar za ta tuka kumbon binciken don ta gudanar da safiyo a kan Mars. Idan shirin ya yi nasara, zai kasance na farko da duniya ta yi nasarar cimma nasarar wadannan manufofi guda uku a aikin binciken duniyar Mars. (Bilkisu Xin)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China