Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Takardar bayani da kasar Sin ta fitar ta sa an kara fahimtar kasar
2019-09-29 16:56:25        cri
Wasu masana sun bayyana takardar bayani da Sin ta fitar a baya-bayan nan, a matsayin wadda ta taimakawa al'ummomin kasashen waje kara fahimtar ci gaban kasar.

Ofishin yada labarai da wayar da kai na majalisar gudanarwar kasar Sin ne ya fitar da wata takardar bayani gabanin bikin cika shekaru 70 da kafuwar Jamhuriyar Jama'ar kasar Sin, wadda aka yi wa taken "Kasar Sin da sauran sassan duniya a sabon zamani", inda ta yi bayani game da ci gaban kasar da hanyar da ta dauka da kuma dangantakarta da sauran sassan duniya.

Ruvisley Gonzalez, malami a cibiyar binciken manufofin kasa da kasa dake Havana, ya ce kasar Sin ta samu ingantacciyar ci gaba a fannin tattalin arziki da zamantakewa, sannan ta samarwa duniya dabarar kulla dangantakar moriyar juna da kuma tsarin samun ci gaba na bai daya ta hanyar tattaunawa da hadin gwiwa.

A nasa bangaren, Stephen Ndegwa, malami a jami'ar kasa da kasa ta Amurka dake Nairobin Kenya, ya ce takardar ta ce kasar Sin ba za ta taba yunkurin amfani da karfi ta yi danniya ba, wanda ke bayyana kudurinta ga duniya.

Ya ce sauran kasashe za su iya koyi da gogewar kasar Sin ta fuskar manufarta ta bude kofa da gyare-gyare da kuma aikin kawar da talauci da inganta rayuwar al'umma.

Shi kuwa Kamal Gaballa, marubuci dan kasar Masar, cewa ya yi, kamar yadda takardar ta bayyana, kasar Sin ta bada gudunmawa wajen kyautata yanayin duniya, kuma shawarar Ziri Daya da Hanya Daya da ta gabatar, bai tsaya ga inganta ci gaban kasar kadai ba, domin ya samar da sabbin damarmaki ga sauran kasashe duniya. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China