Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
NDRC: Babu wasu kamfanoni da suka janye daga kasar Sin
2019-07-17 10:44:47        cri

Mai magana da yawun hukumar raya kasa da yin gyare-gyare ta kasar Sin (NDRC) Meng Wei ya bayyana cewa, har yanzu babu wasu kamfanoni da suka fice daga cikin kasar, a hannu guda kuma manufofin da mahukuntan kasar suka tsara, suna kara janyo hankulan baki masu sha'awar zuba jari na dogon lokaci a cikin kasar.

Meng Wei ya bayyana hakan ne, yayin da yake amsa tambayoyin manema labarai game da rahotanni dake cewa, wai wasu kamfanoni na ficewa daga kasar. Yana mai cewa, galibin kamfanonin dake ficewa daga kasar, kanana ne zuwa matsakaita kuma tasirin ci gaban tattalin arzikin kasar Sin, da bunkasuwar masana'antu da karuwar guraben ayyukan yi, suna tafiya yadda ya kamata.

Jami'in ya ba da misali da manyan canje-canjen dake faruwa a tsarin masana'antu na duniya da ingantuwar masana'antun kasar. Ya ce, ba wani sabon abu ne, wasu masana'antu su bude rassa a kasashen waje.

Ya ce, wasu kamfanoni suna kaura zuwa wurare masu saukin gudanarwa ko wani saboda wani bangare na matakansu na ci gaba na kara shiga kasuwannin duniya, yayin a hannu guda kuma, wani adadi na kananan kamfanonin suka kaura don kaucewa tasirin takaddamar cinikayyar dake tsakanin Sin da Amurka. (Ibrahim Yaya)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China