Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sharhi: Kasar Sin ta mai da hankali sosai kan raya aikin ilimi
2019-09-28 20:44:41        cri
A lokacin kafuwar jamhuriyar Jama'ar kasar Sin a shekarar 1949, kusan kashi 80% na al'ummar kasar ba su taba shiga makaranta ba. Amma bayan wasu shekaru 70, yawan malamai masu aikin koyarwa a kasar ya kai fiye da miliyan 16, kana tsarin ba da ilimin tilas na shekaru 9 ya gama gari a kasar. Wannan ci gaba ya shaida yadda gwamnatin kasar Sin ta yi kokarin raya aikin ilimi a kasar, ganin yadda ta fuskanci matsalar kudi a kokarin raya harkar ilimi a kasar da yawan al'ummarta ya kai fiye da biliyan 1.4.

Amma mai nema yana tare da samu. Bayan da kasar Sin ta gabatar da dokar ba da ilimin tilas a shekarar 1986, sannu a hankali ta tabbatar da wannan tsari na ba da ilimin tilas kyauta ga dalibai wadanda shekarunsu ke tsakanin 6 zuwa 15, a dukkan sassan kasar, bayan shekaru 20 da ta dauka tana kokarin raya wannan tsari. A sa'i daya kuma, an yi kokarin raya harkokin jami'o'i da makarantun koyar da ilimin sana'a a kasar, har ma an samu karin mutanen da suka yi karatun jami'a da suka kai miliyan 270 cikin shekaru 70 da suka wuce.

Bisa manufar kasar Sin, za a kara mai da hankali kan raya masana'antu masu inganci, wadanda ke samar da kayayyaki masu daraja a kasar, inda masu ilimi za su kara taka rawar gani a kokarin taimakawa kasar cimma burinta.(Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China