Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ci gaban da Sin take samu damammaki ne masu kyau ga duniya
2019-09-27 15:56:00        cri
Yau Juma'a gwamnatin kasar Sin ta gabatar da takardar bayani kan Sin da alakarta da sassan duniya a sabon karni, wadda ta waiwayi ci gaban da Sin ta samu tun kafuwarta, da fasahohin da Sin take da su wajen samun bunkasuwa da babbar gudunmawar da Sin take bayarwa ga daukacin duniya, haka kuma ta bayyana alakar Sin da sauran sassan duniya, matakin da ya kuma mayar da martani ga kasashen duniya, kan wasu manyan batutuwa dake jan hankalinsu, kana kuma ya bayyana niyyar kasar Sin na raya duniya cikin lumana da ba da gudunmawarta ga bunkasuwar duniya, da kuma kiyaye zaman oda da doka ta kasa da kasa, matakan da suka bayyana sahihanci da niyyarta da matsayinta na wata kasa dake sauke nauyin dake wuyanta.

To, mene ne dalilin da ya sa Sin ta iya samun bunkasuwa mai armashi? Game da wannan tambaya dake jan hankalin kasa da kasa, takardar ta ba da bayanin cewa, akwai abubuwa biyu masu muhimmanci, na farko, Sin ta fidda wata hanyar samun bunkasuwa mai dacewa. Sabon shugaban babban taron MDD Tijjani Muhammad Bande ya ce, bunkasuwar Sin ta zama abin koyi mai kyau ga sauran kasashe, kuma kasashe masu tasowa ciki hadda Nijeriya na kokarin koyi da kasar Sin.

Na biyu kuwa, babu alaka tsakanin samun bunkasuwa da bin hanyar kama karya. Sin ta fidda wata sabuwar hanya da ta dace wajen samun bunkasuwa cikin lumana da hadin kai da cin moriya tare ta yin la'akari da al'adu masu dogon tarihi da Sin take da su da fahimta mai zurfi kan sharudan da take da su wajen samun muradunta da kuma sanin halin da duniya ke ciki a halin yauzu. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China