Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta samu gagarumin ci gaba a fannin raya wasannin Olympics cikin shekaru 70 da kafuwar sabuwar jamhuriyar kasar
2019-09-27 16:55:03        cri

Gasar Olympics ta shekarar 2022

A ranar 31 ga watan Yulin shekarar 2015 ne dai aka amince birnin Beijing ya karbi bakuncin gasar Olympic ta lokacin hunturun shekarar 2022. Tun daga wannan lokaci ne kuma, birnin na Beijing ya shiga shirin sauke wannan nauyi cikin nasara. Bisa tarihi birnin na Beijing zai kasance na farko a biranen duniya da zai kafa tarihin karbar bakuncin gasar Olympic ta lokacin zafi da kuma hunturu.

Ana fatan gasar ta shekarar 2022, za ta bude wani sabon babi na yayata wasannin kankara ga miliyoyin al'ummar kasar. Za dai a gudanar da wannan gasa mai kunshe da wasanni 109, a birnin Beijing inda za a yi wasannin hockey da zamiyar kankara, da wasannin dusar kankara. Sai kuma birnin Yanqing mai nisan kilomita 80 daga Beijing, inda za a gudanar da wasannin zamiyar kankara na "skiing" da "sliding". Yayin da birnin Zhangjiakou kuma, Zhangjiakou na lardin Hebei mai makwaftaka da Beijing, za a gudanar da Karin wasannin kankara masu yawa dake bukatar tsaunuka da manyan filaye.

A bangaren sufuri kuwa, nan da karshen shekarar nan ta 2019, za a kammala layin dogo na jirage masu saurin tafiya da ya hada birnin Beijing zuwa Zhangjiakou, aikin da bayan kammalar sa, zai rage lokacin tafiya daga Beijing zuwa Yanqing zuwa mintuna 20 kacal, yayin da lokacin tafiya daga Beijing zuwa Zhangjiakou ba zai wuce mintuna 50 ba.

Sababbin wasanni bakwai

Bisa tanajin gasar na 2022, akwai karin wasanni bakwai da za a gudanar a karon farko, ciki hadda wasan motar sunduki ajin mata ko "women's monobob", da "freestyle skiing", da "skating" mai gajeren zango na mutane da yawa, da "Tsallen ski", da "skiing" na kan allon zamani.

Ga birnin Beijing, gasar wasannin Olympic dake tafe a shekarar 2022, zai samar da zarafin karin daidaito a fannin wasanni tsakanin mata da maza, inda ake sa ran shigar karin kaso 45.44 bisa dari, na mata masu wasannin motsa jiki cikin gasar, sama da na adadin irin wannan gasa da ta gabata a baya.

Gasar Olympic ta Beijing ta shekarar 2022, za ta zo daidai lokacin da ake bikin bazara na al'ummar kasar, biki mafi kasaita a kasar Sin, kasancewar za ta fado a watan Fabarairun shekarar ta 2022. Mazauna biranen da za su karbi bakuncin wannan gasa na shirin nishadantuwa daga bikin bazara, ko sabuwar shekarar Sinawa bisa kalandar gargajiya ta kasar. Ko shakka babu gasar za ta samu maraba daga kyawawan al'adun gargajiyar kasar Sin.

Tuni dai aka kaddamar da mutum-mutumin wannan gasa dake tafe. Sunan mutum-mutumin gasar wasannin Olympics na lokacin sanyi na Beijing shi ne "Bing Dwen Dwen", wanda aka tsara fasalinsa bisa siffar dabbar Panda. Mutum-mutumin na shaida irin karfin 'yan wasan motsa jiki, da yadda manufofin wasan Olympics ke karfafa wa jama'a gwiwa.

A daya hannun kuma, sunan mutum-mutumin gasar wasannin Olympics na lokacin sanyi na Beijing na nakasassu na shekarar a 2022, shi ne "Shuey Rhon Rhon", wanda aka tsara fasalinsa bisa siffar fitila. Mutum-mutumin ya nuna cewa, wasannin Olympics na nakasassu, za su taimaka ga samar da duniya mai hakuri da juna, da ra'ayin raya kyakkyawar makomar bil'adama ta bai daya.

Shugaban kwamitin shirya gasar wasannin Olympics na kasa da kasa Thomas Bach ya ce, mutum-mutumin biyu, sun bayyana sigar musamman ta kasar Sin, gami da kyawawan halayen al'ummar kasar, wadanda ko shakka babu, za su zama tamkar fitattun jakadu na gasar wasan Olympics na lokacin hunturu na shekara ta 2022.

Fatan mahukuntan kasar Sin, da daukacin masu sha'awar wasanni, da masharhanta dai bai wuce zuwan lokacin wannan gasa, da gudanar ta cikin nasara ba. A daya bangaren hakan zai sake shaida ikon kasar Sin na sauye nauyin kamrbar bakuncin gasannin kasa da kasa cikin nasara. Kaza lika hakan na kara haskawa duniya irin ci gaba da Sin ke samu a daukacin sassan bunkasa rayuwar bil Adama. (Saminu Alhassan)


1  2  3  

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China