Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta samu gagarumin ci gaba a fannin raya wasannin Olympics cikin shekaru 70 da kafuwar sabuwar jamhuriyar kasar
2019-09-27 16:55:03        cri

Filaye da wuraren wasanni

Karkashin manufar samar da kayan wasa na bukata, ciki hadda gina lambun Olympic, da filayen wasa 37, da wuraren wasanni da za a yi amfani da su a yayin gasar. Wadannan sun hada da gine gine 32 a birnin Beijing, wadanda suka kunshi sababbi 19, da wadanda aka yiwa kwaskwarima 13, da wurare 5 a wasu ragowar sassan kasar Sin daban daban, kamar wurin tseren kwale kwale a Qingdao, da filin wasan kwallo a Tianjin, da Qinhuangdao, da Shenyang, da kuma Shanghai.

Har ila yau Sin ta gina wuraren samar da horo 59, da gine ginen wuraren wasannin nakasassu domin gasannin da suka jibanci haka. Cikin gine ginen da suka dauki hankali akwai filin wasanni na birnin Beijing mai suffar shekarar tsuntsu. Gini ne da ya kasance kunshe da fasahohi masu kayatarwa na zamanin yau, wanda kuma ke da tsarin inganci da zai ba da damar ci gaba da amfani da shi tsawon lokaci bayan kammalar wannan gasa.

Zirga zirga da kayan more rayuwa

Alkaluman kididdiga da mahukuntan kasar Sin suka fitar sun nuna cewa, daga shekarar 2002 zuwa lokacin bude gasar Olympics ta birnin Beijing, birnin ya kashe kudi da yawan su ya kai dala biliyan 1.1 a fannin inganta sashen sufuri, sassan da suka hada da fadada layin dogo na karkashin kasa na birnin Beijing, da kammala layukan sufuri masu hada sassan birane, tare da ginawa ko gyara hanyoyin mota na cikin birnin da tsayin su ya kai kilomita 318, ciki hadda hanyoyi 23 da suka karade sassan filayen da aka gudanar da gasar. Kaza lika an gina sabon wurin sauka da tashin jiragen sama a filin jirage na kasa da kasa dake birnin Beijing.

Fasahohin zamani

"Ya zuwa shekarar 2008, Sin ta kasafta kudi da yawan su ya kai dala biliyan 3.6 a fannin kyautata amfani da fasahohin zamani na sadarwa a birnin Beijing, wannan mataki dai ya haifar da kara yaduwar amfani da yanar gizo mai inganci wajen yada bayanai, da karin amfani da layukan sadarwa masu manyan fasahohi.

Yawon bude ido

Yawan masu yawon bude ido ya yi matukar karuwa cikin sauri, sakamakon shirin gudanar da gasar Olympics. A zahiri take cewa wasanni na jawo ra'ayin masu yawan bude ido. Kafin bude gasar Mr. Chen Jian, shugaban hukumar bincike a fannin tattalin arziki da ya shafi gasar Olympic ta birnin Beijing, ya yi hasashen karuwar baki masu yawon bude ido a lokacin bazarar shekarar ta 2008, zai kai mutum 600,000 baya ga Sinawa da za su yi yawon bude ido a cikin kasar da yawan su ya kai miliyan 2.5. Har ila yau an yi hasashen cewa, yawan baki masu shigowa kasar Sin yawon shakatawa bayan kammalar gasar zai karu daga kaso 8 zuwa kaso 9 a duk shekara. Ita ma hukumar dake lura da harkokin yawon bude ido ta birnin Beijing, ta ce birnin ya karbi baki 'yan yawon bude ido daga kasashen waje miliyan 3.8 a shekarar 2007, adadin da ya karu da kaso 11.8 sama da na shekarar 2006. Bugu da kari, yawan Otal Otal a birnin Beijing sun karu, an kuma yiwa da dama kwaskwarima, yayin da kusan dukkanin sassan nishadantarwa da ayyukan hidima da suka shafi yawon shakatawa suka samu gagarumin ci gaba.

Kyautata yanayin muhalli

Birnin Beijing ya dauki matakai daban daban na kare muhalli. Ciki hadda kara sanya ido kan fitar da iska, ko hayaki mai gurbata yanayi daga masana'antu, an dauki matakan rage kona kwal domin rage fitar da hayaki, an dakatar da wasu manyan gine gine domin rage kura dake shiga sararin samaniya, har ila yau an fitar da wasu manyan masana'antu 200 daga kwaryar birnin Beijing.

Bunkasar tattalin arziki

Tarin yawan jari da ya biyo bayan shirya gasar Olympics na Beijing, ya ingiza tattalin arzikin birnin, bama kawai kwaryar birnin ba har ma da yankunan dake kewaye da shi. Hukumar kididdiga ta birnin Beijing ta ce tun daga shekarar 2002 tattalin arzikin birnin ya ci gaba da karuwa da kaso 2.5 bisa dari.

Kaza lika an samu guraben hadin gwiwa tsakanin birnin Beijing da abokan hulda daga bangaren masu daukar nauyi, da masu samar da kayayyakin wasa, da kamfanoni da dama da suka ci gajiyar shirya wannan gasa. Kafin bude gasar, an yi hasashen sashen tallace tallace na Sin, wanda kafar talabijin ta dauki kaso 42.5 bisa dari, darajar sa za ta daga daga dalar Amurka biliyan 14.7 a shekarar 2007, zuwa dala biliyan 18.4 a shekarar 2008, yayin da talla ta yanar gizo ake hasashen za ta karu da kusan kaso 30 bisa dari.

1  2  3  

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China