Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An harbe dakarun kungiyar IS 8 har lahira
2019-09-09 10:56:17        cri
Bangaren soja na kasar Iraki ya bayyana a ranar 8 ga wannan wata cewa, kawancen kasa da kasa na yaki da kungiyar IS a karkashin jagorancin Amurka ya harbe dakarun kungiyar IS 8 har lahira a jihar Nineveh dake arewacin kasar Iraki a wannan rana.

Sashen bada umurni ga ayyukan hadin gwiwa na kasar Iraki ya bayar da sanarwa cewa, bisa labarin da bangaren soja na jihar Nineveh ya bayar, an ce, kawancen kasa da kasa ya tura jiragen sama inda suka kai hari ga wani sansanin kungiyar IS dake da nisan kilomita 20, kudu da birnin Mosul na jihar, harin da ya hallaka dakarun kungiyar 8 har lahira.

Sashen bada umurnin ya kara da cewa, sojojin kiyaye tsaron kasar Iraki sun kama dakarun kungiyar IS 9 a jihar Salahudin na kasar a wannan rana, wadanda aka shaida cewa suna shirin kai hari ga babban ginin majalisar dokokin jihar, da sojojin kiyaye tsaro.

A watan Disamba na shekarar 2017, kasar Iraki ta sanar da samun nasara a wannan mataki na yaki da kungiyar IS, amma har yanzu akwai wasu masu tsattsauran ra'ayi na kungiyar dake kasar wadanda suke jiran damar sake kai hari. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China