Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Maaikatar tsaron kasar Sin ta shirya bikin murnar cika shekaru 92 da kafa rundunar PLA
2019-07-31 09:47:18        cri

Ma'aikatar tsaron kasar Sin ta shirya wata liyafa a jiya Talata, don murnar cika shekaru 92 da kafa rundunar sojan kwatar 'yancin jamhuriyar jama'ar kasar Sin (PLA) wadda ta fado a ranar 1 ga watan Agusta.

Da yake jawabi a wajen liyafar, mamba a majalisar gudanarwa kana ministan tsaron kasar, janar Wei Fenghe, ya bayyana cewa, har kullum rundunar sojan kasar Sin, za ta kasance mai martaba tsarin shugabancin jam'iyya.

Ya ce, kasar Sin za ta nace ga bin turbar samun bunkasuwa cikin lumana, da aiwatar da manufofinta na tsaron kasa ta hanyar kare kanta, za kuma ta yi aiki tare da sauran kasashen duniya ta yadda za ta ba da gagarumar gudummawa, wajen samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a duniya.

Ministan ya ce, kasar Sin daya ce tak a duniya, kuma Taiwan wani yanki ne na kasar Sin da ba za a iya raba shi ba, ya kuma alkawarta cewa, rundunar PLA za ta tabbatar da tsaron kasa ta hanyar kare 'yanci da cikakkun yankunanta. A hannu guda kuma, rundunar za ta kara zage damtse wajen gina dakarun da babu kamarsu a duniya, za kuma ta shirya bikin murnar cika shekaru 70 da kafa Jamhuriyar jama'ar kasar Sin wadda ta samu manyan nasarori. (Ibrahim Yaya)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China