Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kudin da kasar Sin ta kashe wajen tsaron kanta bai kai na wasu manyan kasashen duniya ba
2019-07-24 14:24:45        cri
Kasar Sin ta fitar da takardar bayanai game da batun tsaron kasa a sabon zamani yau Laraba, inda aka nuna cewa, kudaden da kasar ta kashe a fannin tsaron kasa ya dace da halin da ake ciki.

Ana iya ganin cewa, yawan kudin tsaron kasa da aka kashe a cikin jimillar alkaluman GDP gami da kasafin kudin kasar, da matsakaicin kudin tsaron kasar kan kowane dan kasar, duk ba su kai na wasu manyan kasashen duniya ba. Daga shekara ta 2012 zuwa 2017, yawan kudin da kasar Sin ta kashe wajen tsaron kasa ya kai kimanin kaso 1.3 bisa dari na jimillar GDPn kasar, adadin mafi kankanta a cikin zaunannun kasashe membobin kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya gami da kasar Indiya. Kana, yawan kudin da kasar Sin ta kashe ta fannin tsaron kasa a shekara ta 2017 bai kai daya bisa hudu na Amurka ba.

Yawan kudin da kasar Sin ta kashe ta fannin tsaron kasa zai dace da bunkasuwar tattalin arzikin kasar, wanda zai karu ta hanyar da ta dace kuma yadda ya kamata.(Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China