Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Gwamnatin Rwanda ta gargadi al'ummarta game da zuwa birnin Goma na DRC saboda barkewar Ebola
2019-07-16 10:27:57        cri

Hukumar lafiya ta Rwanda, ta gargadi al'ummar kasar game da zuwa birnin Goma dake gabashin kasar Jamhuriyar Demokradiyyar Congo, wanda ke makwabtaka da kasar ba tare da kwakkwaran dalili ba, biyo bayan barkewar cutar Ebola.

Birnin Goma na kan iyakar kasashen biyu, kuma hukumar kula da shige da fice ta kasar Rwanda ta yi kiyasin mutanen da suka kai 100,000 ne ke tsallake iyakar kasashen biyu a kowacce rana.

Ministar lafiya ta Rwanda, Diane Gashumba, ta bayyana yayin wani taron manema labarai lokacin da take rangadi a kasar cewa, annobar Ebola ba ta kare ba, kuma yanzu ta isa kusa da kasar. Don haka, ta ce akwai bukatar kara yin taka tsantsa da kaucewa ziyartar Goma ba tare da kwakkwaran dalili ba.

Wani limamin Coci da ya yi mu'amala da masu cutar a garin Butembo na arewa maso yammacin Jamhuriyar Demokradiyyar Congo ya kamu da rashin lafiya a baya-bayan nan, kuma ya je Goma cikin motar Bus a ranar 14 ga watan nan, daga bisani aka tabbatar da ya kamu da cutar Ebola. Sai dai, hukumar lafiya ta kasar ta ce barazanar yaduwar cutar a birnin ba ta da yawa.

A wani labarin kuma, an kashe wasu ma'aikatan lafiya biyu a gabashin kasar ta Jamhuriyar Demokradiyyar Congo a karshen makon da ya gabata.

A cewar ma'aikatar lafiya ta kasar, an kashe mutanen biyu da dukkansu suka yi aikin gangamin yaki da barkewar cutar ne a gidajensu dake Kivu ta arewa, bayan an shafe watanni ana musu barazana.

Barkewar cutar ita ce mafi muni da aka samu tun bayan ta barke a kasashen Liberia da Guinea da Saliyo tsakanin shekarar 2014 da 2016, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutane sama da 11,300. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China