Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
WHO da OCHO sun gudanar da taro bayan sabuwar barkewar cutar Ebola a DRC
2019-07-16 09:30:39        cri

Hukumomin MDD da suka hada da hukumar lafiya ta duniya (WHO) da ofishin majalisar dake kula da ayyukan jin kai (OCHA), sun ce taron manyan jami'ai game da sabuwar barkewar cutar Ebola a Jamhuriyar Demokradiyyar Congo da suka yi, ya tabbatar da goyon baya ga jami'an gwamnatin kasar dake aikin tunkarar cutar da sauran shirye-shiryen MDD.

Darakta Janar na WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus, ya ce za su iya kawo karshen cutar da hadin gwiwar gwamnatin kasar. Inda ya ce yanzu suna da ingantattun kayayyakin aiki na tunkarar cutar fiye da da, ciki har da ingantaccen allurar riga kafi.

Sai dai ya ce akwai bukatar kawo karshen duk wani abu dake tarnaki ga aikin tunkarar cutar.

Darakta Janar din ya bayyana haka ne yayin taron da hukumomin biyu suka jagoranci gudanarwa biyo bayan tabbatar da barkewar Ebola karon farko a garin Goma dake gabashin Jamhuriyar Demokradiyyar Congo.

Cikin wata sanarwar hadin gwiwa da suka fitar jiya, MDD ta ce har yanzu barkewar cutar ta tsaya ne a lardunan Kivu ta Arewa da Ituri, amma aikin tunkarar cutar na wani muhimmin mataki. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China