Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Super Eagles ta samu damar shiga jerin kungiyoyi takwas da za su fafata a wasan gaba na AFCON
2019-07-07 16:55:34        cri
Jiya Asabar aka ci gaba da yin gasar cin kofin Afirka wato AFCON na shekarar 2019, a yayin gasar da aka shirya a Alexandria na kasar Masar, kungiyar wasan kwallon kafan Najeriya Super Eagles ta doke kungiyar Kamaru da ci 3 da 2, hakan ya ba ta damar shiga jerin kungiyoyi takwas da za su fafata a wasa na gaba na gasar AFCON, dan wasan kungiyar Odion Ighalo ya kasance dan wasan da ya fi nuna bajinta a wasan bayan da ya yi nasarar zura kwallaye har biyu.

Kana a wannan rana dai aka fafata tsakanin kungiyoyin wasan kasashen Masar da Afirka ta Kudu a birnin Alkahira, inda kungiyar Afirka ta Kudu ta doke Masar da ci 1 mai ban haushi, hakan ya ba ta damar shiga jerin kungiyoyi takwas da za su fafata a wasa na gaba na gasar AFCON, za kuma ta fafata da kungiyar Najeriya a gasar da za a shirya a ranar 10 ga wata. (Bilkisu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China