Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kungiyar kwallon kafa ta Nijeriya ta yi kokari fiye da matsayin da aka ajiye ta cikin jerin kasashen duniya
2019-06-22 15:41:55        cri
Mai horas da Kungiyar kwallon kafa ta mata ta Nijeriya, Thomas Dennerby, ya jaddada a jiya cewa, kungiyar ta yi kokari fiye da matsayin da aka ajiyeta cikin jerin kungiyoyin kasashen duniya da aka yi gabanin zagaye 16 na gasar cin kofin duniya ta mata, inda kungiyar za ta fafata da Jamus.

Sai da Nijeriya ta jira wasan karshe na rukunin da take a ranar Alhamis kafin ta samu gurbi a zageye na 16 na gasar, a matsayin daya daga cikin kungiyoyin 4 mafiya kwazo na dake mataki na 3 a rukunin.

Thomas Dennerby ya bayyanawa manema labarai kafin wasan cewa, sun yi farin ciki sosai da ganin cewa za su buga wasa a zagaye na 16.

Ya kara da cewa, duk da ba su san kungiyar da za su kara da ita ba, kungiyar ta ci gaba da daukar horo a ranar Laraba da Alhamis. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China