Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jaridar Punch ta Najeriya ta wallafa wani sharhi game da jayayyar Sin da Amurka game da cinikayya
2019-06-05 21:08:09        cri

Jaridar Punch da ake wallafawa a tarayyar Najeriya, ta ranar 4 ga watan Yunin nan, ta wallafa sharhin Dr. Tayo Oke, masanin alakar kasa da kasa a Najeriyar, sharhin dake da taken "Danbarwar Huawei da Amurka: hadarin ta ga tattalin arzikin Najeriya ", wanda ya fito da gaskiyar lamari game da yadda Sin ta jima tana cutuwa daga Amurka, a sassa da dama a baya bayan nan, da ma tasirin hakan ga tattalin arzikin Najeriya, kasa mafi yawan jama'a, mafi kuma karfin tattalin arziki a daukacin nahiyar Afirka.

Sharhin ya ce, a bayyane take a fili cewa, nan gaba kadan Sin za ta wuce Amurka a fannin tattalin arziki a duniya. Wannan hasashe ne na hakika da ya shafi tattalin arziki, wanda ke bayyana ga masu ruwa da tsaki dake da tsattsauran ra'ayi a bangarorin, ciki da wajen gwamnatin Amurka. A ganin su, bunkasar tattalin arzikin kasar Sin ba zai yiwu a dakatar da shi ba, amma a kalla, za su iya amfani da rinjayen matsayi na hada hadar cinikayya da Amurka ke da shi, wajen datse fukafukan kasar Sin, wato su saka kasar cikin wani mawuyacin hali, ta yadda kasar ba za ta iya kaiwa ga nasarar zama kasa mafi karfin tattalin arziki ba. Ta wannan mahanga, Sin na shan zargi na aikata laifuka daban daban, da suka jibanci tattalin arziki wadanda hankali ba zai dauka ba, ciki kuwa hadda cuwa cuwar sarrafa kudade, da yiwa hajoji mummunan farashi, da jibge hajoji, da satar fasaha, da kange takara, da kwashewa kasashe masu tasowa albarkatun su, tare da lafta musu bashi, da dai sauran zarge zarge masu yawa.

A cikin sharhin na sa, Dr. Tayo Oke ya kara da cewa, ta hanyar kallon wadannan abubuwa ne za a iya gano matsayin doka, da takaddamar diflomasiyya dake wakana tsakanin Amurka da kamfanin Huawei. A baya bayan nan ma sashen cinikayya na gwamnatin Amurka, ya sanya kamfanin na Huawei cikin "jerin kebantattun sassan sa", wanda hakan ke nufin cewa, dole ne sai kamfanonin kasar Amurka sun nemi izini na musamman, kafin su gudanar da wata mu'amalar cinikayya da kamfanin na Huawei.

Tabbas wannan mataki zai haifarwa kamfanin Huawei babbar matsala ta fuskar kudaden shiga, ba shakka, amma kuma hakan zai sa kamfanin dukufa wajen kirkiro wasu sabbin dabarun maye gurbin hakan. Daga karshe dai, kamar yadda sharhin ya nuna tun da farko, bukatar Amurka ta yiwa Huawei horo, ba wai domin ya karya dokokin tsaron wasu kasashe na daban ba ne, kawai dai dabara ce ta datse fukafukan ci gaban tattalin arzikin kasar Sin, don hana kasar yin tasiri a duniya baki daya, da dakile ta, da hana ta kaiwa ga matsayin da ya dace ta kai.

Sharhin ya kara da cewa, Najeriya za ta makale tsakanin wannan danbarwa, a lokacin da Amurka ta fara nuna mata wadanne kamfanoni na kasar Sin ne take da ikon yin mu'amala da su. Za a iya hana kamfanin Huawei kafa tsarin sa na sadarwa mai kunshe da fasahar 5G a Najeriya, ko da kuwa kyauta zai yi hakan, duba da cewa Amurka ta sanya kamfanin cikin wani kebantaccen jadawali, wanda ake fatan Najeriyar za ta amince da shi. A irin wannan yanayi, kuduri mai muhimmanci ga Amurka, zai zame wa Najeriya asara ta fuskar tattalin arziki.(Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China