Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugabannin Rasha da Amurka sun tattauna ta wayar tarho
2019-05-07 06:51:30        cri

Shugabannin kasashen Rasha Vladimir Putin da na Amurka Donald Trump, sun tattauna ta wayar tarho a jiya Jumma'a, dangane da huldar da ke tsakanin kasashensu da kuma al'amuran kasa da kasa.

Sanarwar da fadar Kremlin ta wallafa a shafinta na Intanet ta ce, shugaba Putin ya tattauna da takwaransa na Amurka Donald Trump ne bisa gayyatar da ya yi masa. Kuma shugabannin 2 sun tattauna kan huldar dake tsakanin kasashensu a yanzu da kuma nan gaba, da hadin gwiwar kasashen ta fuskar tattalin arziki. Dukkansu sun bayyana fatansu na raya huldar tattalin arziki da cinikayya a tsakaninsu domin samun moriyar juna, tare da ci gaba da tattaunawa kan batutuwa da dama, ciki had da tabbatar da zaman lafiya mai dorewa a tsakaninsu.

Sanarwar ta kara da cewa, shugabannin 2 sun yi fatan ci gaba da tuntubar juna a matakai daban daban, kuma dukkansu sun gamsu da tattaunawar, wadda a ganinsu ke da amfani sosai.

Har ila yau Sarah Sanders, kakakin fadar White House ta Amurka ta ce, shugabannin kasashen 2 sun shafe sama da sa'a guda suna tattaunawa ta wayar tarho. Shi ma Shugaba Trump ya bayyana a shafinsa na Twitter cewa, tattaunawar da ya yi da shugaba Putin tana da amfani sosai.

A wani sabon labarin kuma, kafofin yada labaru na Rasha sun ruwaito a jiyan cewa, mataimakin ministan harkokin wajen kasar Sergey Ryabkov ya ce, ministan harkokin waje Sergei Lavrov da takwaransa na Amurka Michael Pompeo, za su tattauna a birnin Rovaniemi da ke arewacin kasar Finland a ranar 6 ga wata, inda za su tattauna halin da ake ciki a kasar Venezuela da dai sauransu. (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China