![]() |
|
2019-06-10 10:36:28 cri |
Yayin da aka kammala bikin gargajiyar kasar Sin na Dragon Boat a ranar Lahadi, hukumar sufurin kasar ta samu dandazon masu zirga-zirga.
An yi hasashen cewa, jiragen kasa za su yi jigilar fasinjoji miliyan 13.7 ya zuwa ranar Lahadi, tare da karin wasu jiragen kasa 889 wadanda aka tanada don amfani da su, kamar yadda hukumar kula da jiragen kasa ta kasar Sin (CRC) ta sanar.
An yi lokacin hutun murnar bikin na Dragon Boat ne tsakanin ranar Jumma'a zuwa Lahadi a wannan shekara.
A ranar 8 ga watan Yuni, sama da fasinjoji miliyan 10.05 ne suka yi zirga-zirga ta jiragen kasa, inda aka tanadi karin jiragen 540 domin biyan muradun matafiyan, in ji hukumar ta CRC.
Kasar Sin ta yi kiyasin fasinjoji miliyan 134 ne za su gudanar da zirga-zirga ta hanyoyin mota da ta ruwa a lokacin bukukuwan, sai dai adadin ya ragu da kashi 3 bisa 100 idan an kwatanta da makamancin lokacin bara, kamar yadda ma'aikatar sufurin kasar Sin ta sanar.
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China