Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Masu Gabatar Da Shirin Telabijin Na Sin Da Amurka Sun Yi Muhawara
2019-05-30 15:19:40        cri

 

 Dangane da tambayar da Regan ta yi mata kan batun shawarwarin da Sin da Amurka suke yi kan lamarin ciniki, Liu Xin ta ce, idan kasar Amurka na da sahihanci, kana ta girmama wakilan gwamnatin kasar Sin, to, ana da imanin ganin wani sakamako mai kyau, saboda yakin ciniki zai yi illa ga dukkan bangarorin 2.

Dangane da batun harajin kwastam, Liu Xin ta ce, ta hanyar rage haraji za a baiwa jama'ar kasashen Sin da Amurka damar sayen kayayyakin juna da kudi mai rahusa. A cewar Malama Liu, a wannan zamanin da muke ciki, ana gudanar da harkokin duniya ne bisa ka'idoji. Idan wani bangare na son canza ka'idojin da ake bi, dole ne ya nemi cimma matsaya da sauran bangarori masu ruwa da tsaki. Bai kamata kasar Amurka ta nuna bambanci ga kasar Sin ba, kana za a dauki matakin rage harajin kwastam ne bisa ra'ayin bai daya na bangarorin biyu. (Bello Wang)


1  2  

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China