Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An bukaci kasashen Afrika su kawo karshen matsalar mutanen da suka kauracewa muhallansu
2019-05-23 09:58:30        cri

An bukaci kasashen Afrika da sauran kungiyoyin Afrika da su lalibo bakin zaren magance matsalar 'yan gudun hijira a Afrika a yayin da nahiyar za ta gudanar da bikin tunawa da ranar Afrika a ranar Asabar.

Yayin da kasashen Afrika za su gudanar da shagulgulan bikin ranar Afrika a Asabar mai zuwa, an bukaci kasashen da su duba hanyoyin magance matsalolin mutanen da aka tilastawa kauracewa muhallansu ke fuskanta wanda ya yi daidai da alkawarin da shugabannin Afrikan suka dauka a baya bayan nan na kawo karshen matsalolin da suka shafi tashe tashen hankula da mutanen da rikici ya daidaita.

A ranar Laraba, hukumar MDD mai kula da tattalin arzikin Afrika (ECA), ta bukaci a kara azama wajen magance dalilan dake haddasa tserewar mutane daga muhallansu, da matsalar 'yan gudun hijira a Afrika, hukumar ta ce, Afrika ta kasance tamkar wata matattara ce ta mutanen da suka kauracewa gidajensu mafi girma a duniya.

A bisa ga alkaluman da hukumar ta ECA ta fitar, sama da kashi 1 bisa 3 na yawan mutane miliyan 68 da aka tilastawa ficewa daga muhallansu a fadin duniya suna nahiyar Afrika.

Tashe tashen hankula, take hakkin dan adam, bala'o'i, matsanantan matsalolin kiwon lafiyar al'umma, da halin kunci da al'umma ke fadawa, suna daga cikin manyan dalilan dake tirsasa mutane kauracewa gidajensu a nahiyar Afrika, in ji hukumar ta ECA.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China