logo

HAUSA

Majalissar Wakilan Jama’ar Kasar Sin Ta Yi Allah Wadai Da Dokar Da Amurka Ta Kafa Mai Lakabin “Haramta Tilastawa Al’ummar Uygur Kwadago”

2021-12-24 20:29:25 CRI

Majalissar Wakilan Jama’ar Kasar Sin Ta Yi Allah Wadai Da Dokar Da Amurka Ta Kafa Mai Lakabin “Haramta Tilastawa Al’ummar Uygur Kwadago”_fororder_xj02

Kwamitin dake lura da harkokin waje, na majalissar wakilan jama’ar kasar Sin, ya yi Allah wadai da dokar da Amurka ta kafa, mai lakabin “haramta tilastawa al’ummar Uygur kwadago”.

Wata sanarwar da kwamitin ya fitar a Juma’ar nan, ta bayyana dokar da Amurka ta kafa, a matsayin matakin tsoma baki cikin harkokin cikin gidan Sin, ta hanyar fakewa da ‘yancin bil Adama.

Kaza lika sanarwar ta ja kunnen Amurka da cewa, muddin ta nacewa bin wannan mummunar hanya, ba shakka Sin za ta mayar da martani mai karfi da ya dace.     (Saminu)

Saminu